settings icon
share icon
Tambaya

Mece ce ma’anar rayuwa?

Amsa


Mece ce ma’anar rayuwa? Yaya zan iya sami manufa, cikawa, da biya muradi cikin rayuwa? Ko zan sami iyawa na kammala wani abu da daɗewa mai ma’ana? Mutane da dama basu taɓa daina tunani mece ce rayuwa take ba. Sun dubi shekarun baya na ƙarshe kuma da yin mamaki yadda dangantakarsu ta faɗi warwas da dalilin da suna ji kamar wofi ko da yake mai yiwuwa ne sun kai ga abin da sun nufa su kammala. Wani mai wasan baseball (wata irin wasa) wanda yayi fice zuwa babban ɗaki fitattun wasan baseball an tambaye shi mene ne ya so da wani ya gaya masa sa’anda da farko ya fara yin wasan basaball. Ya amsa, “Na so cewa da wani ya faɗa mani cewa sa’anda ka kai ƙololuwa, babu wani abu a wurin.” Maƙasudai da dama sun bayyana rashin kome nasu kawai bayan an ɓad da shekaru cikin bin su.

A cikin jam’iyyarmu na ɗan adam, mutane suna bi manufofi da dama, da tunani cewa a cikinsu zasu sami ma’ana. Waɗansu daga waɗannan abubuwan da ake bi sun haɗa: nasara a ciniki, wadata, dangantaka mai kyau, jinsi, nishaɗi, yin alheri ga waɗansu, da dai sauransu. Mutane sun shaida cewa yayinda suka cim ma manufofinsu na arziki, dangantaka, da jin daɗi, an sami har yanzu dai wofi mai zurfi ne a ciki- ji na wofi da babu kome da alama zai cika ta.

Marubucin Littafi Mai Tsarki na Mai Hadishi yana furta wannan ji sa’anda ya faɗi, “ Banza a banza ne!... dukan kome banza ne.” Wannan marubuci yana da wadata fiye da kima, hikima a gaban wani mutum na zamanin sa ko tamu, ɗarurrukan mata, fadodi da kuma lambuna da suka zama abin kyashin mulkoki, abin ci da giya mafi kyau, kuma yana da kome na siffar nishaɗi samamme. Kuma ya faɗi a wani karo, cewa kome da zuciyar sa ta so, ya bi abin. Kuma duk da haka ya taƙaita “ rayuwa a ƙarƙashin rana” (ayi rayuwa sai kace duk abin da ke akwai ga rayuwa shine abin da zamu iya gani da idanun mu da kuma ji da azancin mu) ya zama banza ne! Me yasa akwai wofi irin haka? Domin Allah ya halicce mu don wani abu a gaban abin da zamu iya ji a ciki nan da yanzu. Sulemanu ya faɗi game da Allah, “ Shi kuma ya sanya tunanin lahira a cikin zukatan mutane ...” A cikin zukatan mu muna da sane cewa wannan “nan-da-yanzu” ba ita ce duk abin da ke akwai ba.

A cikin Farawa, littafin farko na Littafi Mai Tsarki, muna ganin cewa Allah ya halicce ɗan adam cikin surar sa (Farawa 1:26). Wannan na nfin cewa mun fi kama da Allah da muke kama da kome na dabam (kowace siffar rai dabam). Mun kuma iske cewa kamin ɗan adam ya faɗi cikin zunubi da la’ana tazo kan duniya, waɗansu abubuwa sun zama gaskiya: (1) Allah yayi mutum taliki mai zama da jama’a (Farawa 2:18-25); (2) Allah ya baiwa mutum aikin yi (Farawa 2:15); (3) Allah yayi zumunci da mutum (Farawa 3:8); kuma (4) Allah ya bai wa mutum mulki bisan duniya (Farawa 1:26). Mene ne muhimmancin waɗannan abubuwa? Na gaskata cewa Allah ya nufe mu kowannen mu da ƙarin don cikar rayuwar mu, amma duk waɗannan (musamman zumuncin mutum da Allah) sun gamu da cikas ta faɗuwar mutum cikin zunubi da sakamakon la’ana bisa duniya (Farawa 3).

Cikin Wahayin Yahaya, littafin ƙarshe na Littafi Mai Tsarki, a ƙarshen abubuwa da dama na ƙarshen zamani, Allah ya bayyana cewa zai hallakar da duniya ta yanzu da sammai kanda mu san su da kuma shigo da madawwamin zamani ta halittar sabuwar sama da sabuwar duniya. A lokaci nan, zai maido da cikakken zumunci da fansasshen ɗan adam. Waɗannan ƴan adam za a shar’anta su da rashin cancanta da jefar wa cikin Tafkin Wuta (Wahayin Yahaya 20:11-15). Kuma la’anar zunubi za a kawar; babu sauran zunubi, baƙin ciki, ciwo, mutuwa, zafi, da da sauran su (Wahayin Yahaya 21:4). Kuma masu bada gaskiya zasu gaji dukkan abubuwa; Allah zai zauna tare da su, kuma zasu zama ƴaƴan sa (Wahayin Yahaya 21:4). Hakanan, mun kawo ga cikakken da’ira, nufin Allah ya halicce mu mu sami zumunci da shi; mutum yayi zunubi, ya tsinke zumunci nan; Allah ya maido da cikakken zumunci nan cikin madawwamin zamani tare da waɗancan da ya tsammaci sun cancanta masa. Yanzu, a bi ta cikin rayuwa a sami kome da kome kaɗai a mutu rabe da Allah na har abada ya zama mafiya muni da banza! Amma Allah yayi wat hanya ba kaɗai ya sa jin daɗi ainun na har abada ta yiwu ba (Luka 23:43), amma kuma wannan rai mai biyan muradi da mai ma’ana kuma. Yanzu, yaya wannan jin daɗi na har abada kuma da “aljanna anan duniya” zai samu?

MAYAR DA MA’ANAR RAYUWA TA WURIN YESU KIRISTI

Kamar yadda anyi hasashe a sama, ma’ana ta ainihi daga yanzu da har abada na samuwa ne a cikin maido da zumuncin wani da Allah wanda ta bata a yayin faɗuwar Adamu da Hawwa’u cikin zunubi. Yau, zumuncin nan da Allah kaɗai na yiwuwa ne ta wurin Ɗan sa , Yesu Kiristi (Ayyukan Manzanni 4:12; Yahaya 14:6; Yahaya 1:12). Ana ribato rai madawwami sa’anda wani ya tuba daga zunubin sa/ta (ba a so kuma a ci gaba cikin ta amma ana son Kiristi ya canza su da kuma maishe su sabuwar mutum) da fara dogara wa kan Yesu Kiristi a matsayin mai Ceto ( dubi tambaya “Mece ce Shirin Ceto?” don ƙarin bayyani kan wannan fito mafi muhimmanci).

Yanzu, rayuwa mai ma’ana ta ainihi ba ta samuwa kawai cikin gano Yesu a matsayin mai ceto ba (da ban mamaki da haka take). Alhali, ainihin ma’ana rayuwana samuwa ne yayin da wani ya fara bin Kiristi a matsayin almajirin sa, yana koyo daga gare shi, yana kashe lokaci tare da shi cikin maganar sa, Littafi Mai Tsarki, yana sadarwa da shi cikin addu’a, da kuma tafiya da shi cikin biyayya ga dokokin sa. Idan kai mara bada gaskiya (ko watakila sabuwar tuba) kana mai yiwuwa ce ma kanka, “sautin bai tada mani hankali ainun ko biyan wani muradi ba)!” Amma don Allah ka karanta zuwa gaba da ɗan kaɗan kawai. Yesu ya faɗi waɗannan furce-furce:

“Kuzo gare ni dukkanku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku. Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali’u ne, marar girman kai, zaku kuma sami kwanciyar rai. Domin bautata sassauƙa ce, kaya na kuma marar nauyi ne.” (Matiyu 11:28-30). “Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace” (Yahaya 10:10b). “Duk mai son bi na, sai ya ƙi kansa, ya dauki giccyen sa, ya bi ni. Duk mai son tattalin ran sa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ran sa saboda ni, zai same shi” (Matiyu 16:24-25). “Ka nemi farin cikin ka a wurin Ubangiji, zai kuwa biya maka bukatar ka” (Zabura 37:4).

Abin da duk waɗannan ayoyi ke faɗi shine cewa muna da zaɓi. Zamu iya ci gaba da neman jagorar rayukan mu (da sakamakon na yin rayuwar wofi) ko zamu iya zaɓa mu bi Allah da nufin Sa don rayukan mu da dukkan zuciya (wanda zai zo da sakamakon yin rayuwa mai falala, samun biyan muradin zuciyar ka, da wadatuwa da biyan bukata). Wannan haka yake saboda Mahaliccinmu yana ƙaunar mu kuma yana begen mafi kyau domin mu (ba lalle lalle rayuwa mafi sauƙi ba ne, amma mafi biyan muradi).

A ƙarshe, ina so in gwada kwatance da nayi aro daga wani aboki Fasto. Idan kai mai son wasanni ne kuma ka yanke shawara kaje kallon wata wasa ta gwanaye, zaka iya cabko ƴan daloli kuma ka sami wurin zama da “haɓo” a layuka na sama a babban filin wasanni ko zaka iya fitar da ƙalilan ɗarurrukan daloli kuma ka zauna can kasa kuma kana gab da wasan. Haka ne yake a cikin rayuwar Kirista. Ganin aikin Allah MURARAN bai zama na Kiristoci na ran Lahadi ba ne. Ba sa biyan farashi ba. Ganin aikin Allah MURARAN na almajirin Yesu da dukkan zuciya ne wanda da gaske ya tsai da bin muradin kansa/ta cikin rayuwa don shi ko ita ta iya bin manufofi Allah cikin rayuwa. SUN biya farashi (cikakken sallamar wa ga Kiristi da nufin Sa); suna yin zaman rayuwa da cikamakin ta; kuma zasu iya fuskanci junan su, mutum ɗan’uwansu, da kuma Mahaliccin su banda da na sani! Ko ka biya farashi? Kana son kayi ɗin? Idan haka ne, ba zaka yunwata da neman ma’ana ko manufa kuma ba.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mece ce ma’anar rayuwa?
© Copyright Got Questions Ministries