settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da dinosaurs? Akwai dinosaurs cikin Littafi Mai Tsarki?

Amsa


Batu na dinosaurs cikin Littafi Mai Tsarki ya zama sashi na gardama mafi girma da ake yi cikin jama’ar Kirista akn daɗewar shekarun duniya, madaidaiciyar fassara na Farawa, da kuma yadda za a fassara shaidun waje da muke samunsu kewaye da koina. Waɗanda sun gaskata da shekara mafi daɗewa ga duniya sun faye yarda cewa Littafi Mai Tsarki bata ambaci dinosaurs ba, don bisa ga samfurinsu , dinosaurs sun mutu miliyoyin shekaru kafin mutum na farko ya taɓa yi tafiya a duniya. Mutane da suka rubuta Littafi Mai Tsarki basu iya ganin dinosaurs a raye ba.

Waɗanda sun gaskata cikin shekaru mafi ƙanƙanta na duniya sun faye yarda cewa Littafi Mai Tsarki ta ambaci dinosaurs ko da yake bata taɓa cikin gaskiya yi amfani da kalmar “dinosaurs.” Maimako, ta mori kalmar Ibraniyanci tanniyin. An juya Tanniyin da hanyoyi ƴan kaɗan cikin Littattafan mu Masu Tsarki na Turanci; wasu lokatai ya zama “dodon ruwa,” wasu lokatai ya zama “maciji.” Ana yawan juya shi “dragon.” Tanniyin tana nan da kamar wata irin ƙato ja-ciki. Waɗannan halittu an ambace kusan sau talatin cikin Tsohon Alƙawari kuma suna samuwa duk kan ƙasa da kuma cikin ruwa.

Kuma ana ambaton waɗannan ƙaton ja-ciki duka kusan sau talatinn koina a Tsohon Alƙawari, Littafi Mai Tsarki ta kwantata waɗansu halittu cikin hanyar da wasu masana suka gaskata marubuta mai yiwuwa na kwatanta dinosaurs ne. Behemoth (dorina) ana cewa ita ce mafi ƙarfi dukka na halittar Allah, ƙatoto da ana gwada wutsiyarta da itacen al’ul (Ayuba 40:15 da na biye). Wasu masana sun ƙoƙarta su kamanta Behemoth kamar ko giwa ko dai dorina ne. Wasu kuwa suna cewa giwaye ko su dorina suna da siraran wutsiyoyi ainun, ba kome da za a kwatanta da itacen al’ul ba. Dinosaurs kamar Brachiosaurus da kuma Diplodocus a wata fanni suna da ƙattin wutsiyoyi waɗanda za a iya da sauƙi a kwatanta da itacen al’ul.

Kusan kowace wayewar kai ta zamanin da suna da wata irin zane mai nuna hoton halitta masu ja-ciki. Petroglyphs, kayan tarihi da ma ƙananan siffofin yumɓu da aka same su a Amirka ta Arewa suna kama da hotunan zamani na dinosaurs. Sassaƙan duwatsu cikin Amirka ta Kudu na nuna hoton mutane na hawan halittun irin kamar da na Diplodocus kuma, abin mamaki, suna da sanannun surorin irin na Triceratops-, Pterodactyl- da Tryannosaurus Rex. Zanen hotunan Romawa, kayan yumɓu na manya da bangayen birnin Babila duk sun shaida ma’amalar al’adar ɗan adam, a labarin ƙasa- waɗancan halittu ba iyaka da ban sha’awa suke, Nitsattsen bayyanai kamar na Marco Polo’s II Milione sun haɗu da tatsuniyoyin almara na dabbobi masu ɓoye dukiya. Rahotannin zamanin yau na hange –hange sun dage ko da yake ana ɗauke su kullum da shakku ƙwarai.

A ƙari da gundarin adadi na shaidun zuriyar bani adam da tarihi na zaman tare da dinosaurs da mutum, akwai wasu shaidun waje kuma, kamar su daɗaɗɗun zanen tafin ƙafaffun mutane da na su dinosaurs da an gano tare a wurare cikin Amirka ta Arewa da Yamma-Tsakiyar Asiya.

Haka nan, akwai dinosaurs cikin Littafi Mai Tsarki? Batun tayi nesa daga shiryawa. Ya dangana ga yadda kake fassarta shaidun da ke akwai da yadda kana duban duniyar da ke kewaye da kai. Anan a Gotquestions.org mun gaskata da fassarar ƙaramar duniya da yarda cewa dinosaurs da mutum sun kasance tare. Mun gaskata cewa dinosaurs sun mutu a wani lokaci bayan ruwan tsufana bisa dalilan kai kawo na halin zaman mutum da gaskiyar cewa mutum kullum na farautarsu daga kau dasu daga doron duniya.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da dinosaurs? Akwai dinosaurs cikin Littafi Mai Tsarki?
© Copyright Got Questions Ministries