settings icon
share icon
Tambaya

Ya kamata mataye suyi hidima a matsayin fastoci/masu wa’azi? Mene ne Littafi Mai Tsarki ke fadi game da mataye cikin ma’aikatar bishara?

Amsa


Akwai watakila babu wata batu mafi gardama cikin Ikilisiya yau banda batun mataye cikin hidima a matsayin fastoci/masu wa’azi cikin ma’aikata. A sakamakon haka, yana da muhimmanci ainun da kar a dubi wannan batun da kamar mazaje da mataye ne. Akwai matayen da sun gaskata cewa kar mataye su yi hidima a matsayin fastoci kuma cewa Littafi Mai Tsarki tasa abubuwan taƙurawa kan ma’aikatar mata- kuma akwai mazajen da sun gaskata cewa mataye zasu iya yin hidima a matsayin masu wa’azi da kuma cewa babu abubuwan taƙurawa kan mataye cikin ma’aikata. Wannan ba wani batu na jinsi ko na nuna tara bane. Ya zama wata batun fassarar Littafi Mai Tsaki ne.

1Timoti 2:11-12 tana sanar, “Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya. Ban yarda mace ta koyar, ko kuma tayi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru.” A cikin Ikilisiya, Allah ya bai wa aikin yi ga mazaje da mataye. Wannan sakamako ne ta hanyar da aka halicci dan adam (1Timoti 2:14) da hanya ta yadda zunubi ya shigo duniya (2Timoti 2:14). Allah, ta wurin rubutun Manzo Bulus, ya taƙura wa mataye daga yin hidima cikin ayyukan ruhaniya na ikon koyarwa bisa mazaje. Wannan ya cire mataye daga hidima a matsayin fastoci, wanda tabbatacce ya shafi yin wa’azi ga, koyarwa, da kuma samun ikon ruhaniya bisa kan mazaje.

Akwai “rashiin yarda” da yawa ga wannan ra’ayi na mataye cikin ma’aikata/fastoci mataye. Na gama-gari shine cewa Bulus ya taƙura wa mataye daga koyarwa domin a cikin ‘ƙarni na farko, yawancin mataye marasa ilimi ne. Duk da haka, 1Timoti 2”11-14 babu inda ta ambaci matsayin rashin ilimi ba. Idan da ilimi ne ya zama ma’auni don aiki a ma’aikata, da yawa na almajiran Yesu da ya yiwu da basu sami cancanta ba. Rashin yarda na gama-gari na biyu shine cewa Bulus ya taƙura wa Afisawa kaɗai daga yin koyarwa (Timoti ta ɗaya an rubuta wa Timoti ne, wanda ya zama fasto na Ikilisiyar cikin Afisa). A san da birnin Afisa don haikalinta ga Atamis, allahiya ta ƙarya na Girikawa/Romawa. Mataye ne ke da iko cikin sujadar Atamis. Duk da haka, littafin Timoti na 1 babu inda ta ambaci Atamis ba, ko ma a ce Bulus ya ambaci sujadar Atamis a matsayin dalili na taƙura wa cikin 1Timoti 2:11-12).

Rashin yarda na gama-gari na uku shine cewa Bulus kaɗai na zancen mazaje da mataye ma’aurata ne, ba na maza da mata dukka ba ne. Kalmomin yaren Girika cikin 1Timoti 2:11-14 suna iya magana ga mazaje da mataye ma’aurata. Duk da haka, ma’anar asali na kalmomin sune mazaje da mataye. Wani kuma, kalmomin Girika iri ɗaya ne aka mora cikin ayoyi 8-10. Mazaje ne kaɗai ke daga hannaye sama masu tsarki cikin addu’a banda fushi da jayayya (aya8)? Mataye ne kaɗai zasu yi ado da dama-dama, su zama da ayyuka nagari, da kuma yi wa Allah sujada (ayoyi 9-10)? Ko kaɗan ba haka bane. Ayoyi 8-10 a fili na magana ga mazaje da mataye dukka ne, ba ga mazaje da mataye ma’aurata ba. Babu wani a cikin wurin da zai zamanto an tsallaka ga mazaje da mataye ma’aurata cikin ayoyi 11-14 ba.

Duk da haka wani rashin yarda na kullum ga wannan fassara na fastoci mataye/masu wa’azi ya dangane da Maryamu, Debora, Hulda, Priskila, Fibi da dai sauransu, - matayen da sun riƙe matsayin shugabanci cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan rashin yarda ya gaza lura da wasu muhimman abubuwa. Dangane da Debora, ita ce kaɗai na mace muhunkuciya tsakanin maza mahukunta 13. Dangane da Hulda, ita ce kaɗai na mace annabiya tsakanin ɗumbun mazaje annabawa da aka ambata cikin Littafi Mai Tsarki. Abin da kaɗai ya haɗa Maryamu da shugabanci shine don zamanta ƴar’uwar Musa da Haruna. Mataye biyu mafi fice a lokacin sarakuna sune Ataliya da Yezebel – da kyar suka misalta irin shugabancin da Allay yake so.

A lokacin littafin Ayyukan Manzanni, sura 18, Priskila da Akila an nuna su a matsayin amintattun ma’aikatan Kiristi. Ana ambaton sunan Priskila da farko, mai kamar da cewa ita ta fi “fice” cikin ma’aikata fiye da mijinta. Duk da haka, babu inda aka kamanta Priskila da sa kai cikin aikin ma’aikata da yayi saɓani da 1Timoti 2:11-14. Su Priskila da Akila suka kawo Afolos zuwa gidansu da kuma duk sun almajirtar da shi, an bayyan masa Maganar Allah mafi madaidaici (Ayyukan Manzanni 18:26).

A cikin Romawa 16:1, ko da idan Fibi an ɗauke ta ‘mai hidima” maimakon “baiwa” – wannan bai nuna cewa Fibi ta zama malama cikin Ikilisiya ba. “Gwanin koyarwa” an bayar ne a matsayin cancanta ga dattijai amma ba ga masu hidima ba (1Timoti 3:1-13; Titus 1:6-9). Dattijai/masu kula da Ikilisiya (Bishop)/ da masu hidima an kamanta su da “miji mai mata ɗaya,” “wanda ƴaƴansa ke masu bada gaskiya” da kuma “ya zama marar abin zargi.” Bugu da ƙari, cikin 1Timoti 3:1-13 da Titus 1:6-9, wakilin sunaye na fannin zikili ne gaba ɗaya aka ambaci dattijai/masu kula da Ikilisiya/da masu hidima.

Tsari na 1Timoti 2:11-14 ta mai da “dalilin” cikakke sarai. Aya ta 13 ta faru da “Gama” kuma ta bada “sanadi” na abin da Bulus ya faɗa cikin ayoyi 11-12. Me yasa mata ba zasu yi koyarwa ko samun iko akan mazaje? Saboda- “Ai, Adamu aka fara halitta , sa’anan Hawwa’u. Ba kuma Adamu aka yaudara ba, matar ce aka yaudara har ta ƙeta umarni” wannan ne dalilin. Allah ya halicci Adamu da farko kuma sai ya halicci Hawawa’u ta zama “mataimakiya” ga Adamu. Wannan tasrin halitta tana da shafa na gama-duniya ga abin ga bani adam cikin iyali (Afisawa 5:22-33) da kuma ikilisiya. Gaskiyar cewa Hawwa’u ce aka ruɗar ta zama wani dalili ga mata kar su zama fastoci ko samun ikon ruhaniya a bisa mazaje.

Wannan zai kai wasu ga gaskata bai kyautu su koyar ba don da sauƙi a ruɗar da su. Wancan tunani abin gardama ne---amma idan mataye da sauƙi a ruɗar dasu, me yasa za a yarje masu su koya wa yara (waɗanda da sauƙi ne su ruɗu) da waɗansu mataye ( waɗanda an ɗauka suna ruɗuwa da sauƙi)? Ba abin da nassin ke faɗi ba ke nan. Mataye ba zasu yi koyarwa ba ko su sami ikon ruhaniya akan mazaje saboda Hawwa’u ce aka ruɗar. A sakamako, Allah ya riga ya ba mazaje da farko ikon koyarwa cikin Ikilisiya.

Mataye sun faye cikin baye-bayen karamci, jinkai, koyarwa da taimakai. Da yawan aiwatarwa na ikilisiya ya dogara ne kan mataye. Mataye a cikin Ikilisiya ba a taƙura masu ga addu’a cikin jama’a ko yin annabaci (1Korantiyawa 11:5), sai kaɗai ga samun ikon koyarwar ruhaniya a bisa mazaje ne. Babu inda Littafi Mai Tsarki ta taƙura wa mataye daga yin amfani da baye-bayensu na Ruhu Mai Tsarki ba (1Korantiyawa Sura 12). Mataye, daidai kamar da mazaje, an kiraye su ga yiwa wasu hidima, a nuna ɗiyan Ruhu (Galatiyawa 5:22-23), kuma ayi shela Bishara ga ɓatattu (Matiyu 28:18-20; Ayyukan Manzanni 1:8; 1Bitrus 3:15).

Allah ya naɗa cewa mazaje ne zasu yi aiki a gurabun iko na koyarwar ruhaniya a cikin ikilisiya. Wannan ba don mazaje ne lalle sun fi zama malamai masu kyau ba, ko don mataye sun gaza da daraja ko basira ba (wanda ba shi ne ba). Ya zama kawai yadda Allah ya tsara gudanarwa ne. Ya kamata mazaje su nuna gurbi cikin shugabancin ruhaniya – cikin rayuwarsu da ta wurin maganganunsu. Mataye ya kamata su ɗauki matsayin da ya gaza da iko. Ana ƙarfafa mataye su koyar wa wasu mataye (Titus 2:3-5). Littafi Mai Tsarki kuma bata taƙura wa mataye daga koyar wa yara ba. Aikin da kaɗai an taƙura wa mataye daga yi shine koyarwa ko samun matsayin ruhaniya a bisa kan mazaje. Wannan bisa hankali zai kunsa fastoci mataye/masu wa’azi. Wannan bai mai da mataye da rashin muhimmanci ba, ko ta halin ƙaƙa, amma alhali kuwa ya basu aiki mafi zura ido mai jituwa da yadda Allah ya basu baiwa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ya kamata mataye suyi hidima a matsayin fastoci/masu wa’azi? Mene ne Littafi Mai Tsarki ke fadi game da mataye cikin ma’aikatar bishara?
© Copyright Got Questions Ministries