settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da jarfa/ hujin jiki?

Amsa


Dokar Tsohon Alkawari ta umarci Isra’ilawa, “ko ku tsattsaga jikinku, ko kuyi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji” (Littafin Firistoci 19:28). Hakanan, ko da yake masu bada gaskiya a yau basa ƙarƙarshin dokar Tsohon Alƙawari (Romawa 10:4; Galatiyawa 3:23-25; Afisawa 2:15), gaskiyar cewa da ma akwai doka gaba da jarfa ya isa ya sa mu tambaya. Sabon Alƙawari bata ce kome ba game da ko mai bi ya kamata ko bai kamata yayi wa kansa jarfa.

Dangane da jarfa da hujin jiki, gwadawa mai kyau shine a ƙudura ko da gaske zamu iya, da nazarin lamiri, tambayi Allah ya albarkaci kuma ya mori wata aiki takamaimai don manufofin sa mai kyau. “To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, kuyi kome saboda ɗaukakar Allah” (1Korantiyawa 10:31). Littafi Mai Tsarki bata yi doka gaba da jarfa ba ko hujin jiki, amma kuma bata bamu kowane dalili da zamu gaskata Allah zai yarda mana zama da jarfa ko hujin jiki ba.

Wani batu da zamu duba shine ado mai dama-dama. Littafi Mai Tsarki ta umarce mu da muyi ado mai dama-dama (1Timoti 2:9). Wata ɓangaren ado mai dama-dama shine a tabbatar cewa kome da ya kamata a rufe da zane na nan a rufe sosai. Duk da haka, asalin ma’anar dama-dama ba a jawo hankali gare ka ba. Mutane masu yin ado mai dama-dama suna ado haka ɗin ne cewa basa hankali ga kansu ba. Jarfa da hujin jiki mafi tabbaci na jawo hankali. A cikin wannan azanci, jarfa da hujin jiki ba su a dama-dama ba.

Ƙa’idar Littafi Mai Tsarki mafi muhiimmanci kan waɗannan batuttuwa da Littafi Mai Tsarki ba ta yi maganarsu musamman ba shine cewa idan akwai damar shakka kan ko abin ya gamshi Allah, to ya zama mafi kyau kar mu sa kanmu cikin wancan aiki. “ Duk abin da bana bangaskiya ba ne, zunubi ne” (Romawa 14:23). Muna bukata mu tuna cewa jikunanmu, har ma da rayukanmu, an fansa kuma na Allah ne. Duk da haka, 1Korantiyawa 6:19-20 bai shafi kai tsaye ga jarfa ko hujin jiki ba, ta dai bamu wata ƙa’ida ne, “Mene ne?” “Ashe, ba ku sani ba, jikinku haikali ne na Ruhu Mai Tsarki wanda ke zuciyarku, wanda kuka samu a gun Allah? Ai, ku ba mallakar kanku bane. Sayenku aka yi da tamani. To, sai ku ɗaukaka Allah da jikinku” Wannan gaskiya mai girma kamata ya sami ainihin ɗaurewa kan abin da muke yi da inda muke tafiya tare da jikunanmu. Idan jikunanmu na Allah ne, kamata yayi mu tabbatar mun sami “iznin” sa sosai kafin mu “zazzana ta” da jarfa ko da hujin jiki.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da jarfa/ hujin jiki?
© Copyright Got Questions Ministries