settings icon
share icon
Tambaya

Yaya zan iya san banda shakka cewa kana da rai madawwami kuma da cewa zaka je sama sa’anda ka mutu?

Amsa


Ko ka san banda shakka cewa kana da rai madawwami kuma da cewa zaka je sama sa’anda ka mutu? Allah yana son ka zama da tabbaci. Littafi Mai Tsarki tana cewa:”Na rubuto maku wannan ne, ku da kuka gaskata da suna Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami” (1Yahaya 5:13). Kamar a ce kana tsaye a gaban Allah daidai yanzu kuma Ya tambaye ka,”Me yasa zan yarda maka shiga cikin Sama?” Me zaka ce? Mai yiwuwa ba zaka san abin da zaka amsa ba. Abin da kake bukata ka sani shine cewa Allah yana ƙaunar mu kuma ya tanadar mana hanyar da zamu san tabbatacce inda zamu zauna har abadan abadin. Littafi Mai Tsarki ta bayyana kamar haka:” Saboda ƙaunar da Allah yayi wa duniya har ya bada makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai mdawwami” (Yahaya 3:16).

Mu da farko sai mun fahimce matsalar da yake hana mu daga shigar sama. Damuwar ita ce wannan – halin mu na zunubi shine mai hana mu daga samun wata dangataka tare da Allah.

Mu masu zunubi ne bisa hali da zaɓi.” Gama ƴan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah” (Romawa 3:23). Ba zamu iya ceton kanmu ba.” Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba kokarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah, ba kuwa saboda aikin lada ba, kada wani yayi fariya” ( Afisawa 2:8-9). Mun cancanci mutuwa da jahannama” Gama sakamakon zunubi mutuwa ne” (Romawa 6:23).

Allah mai tsarki da adalci kuma dole ne ya hori zunubi, duk da haka yana ƙaunarmu kuma ya tanadar mana da gafarar zunubi. Yesu yace:”Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yahaya 14:6). Yesu ya mutu dominmu a bisa giccye:” Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba kari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah” (1 Bitrus 3:18). An tashe Yesu daga matattu:” Wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi domin mu sami kuɓuta ga Allah” (Romawa 4:25).

Haka, koma ga tambaya na asali –” Yaya zan iya sani da tabbas cewa zan je sama sa’anda na mutu? Amsar ita ce wannan – gaskata cikin Ubangiji Yesu Kiristi kuma zaka sami ceto (Ayyukan Manzanni 16:31).” Amma duk iyakar wadanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa, ya basu ikon zaman ƴaƴan Allah” (Yahaya 1:12). Zaka iya karɓi rai madawwami a matsayin KYAUTAR baiwa.”Baiwar Allah ita ce rai madawwami ne cikin Kiristi Yesu Ubangijin mu” (Romawa 6:23). Zaka iya yin cikakken rayuwa da rayuwa mai ma’ana yanzu-yanzu nan. Yesu ya ce:” Ni kuwa na zo ne domin su sami rai, su kuma same shi a yalwace” (Yahaya 10:10). Zaka iya zama tare da Yesu cikin sama har abadan abadin, gama yayi alƙawari:” In kuwa na je na shirya maku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, kuma ku zama kuna can” (Yahaya 14:3).

Idan kana son ka karɓi Yesu kiristi a matsayin mai cetonka ka kuma karɓi gafartawa daga Allah, ga addu’ar da zaka iya yi. Faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto.”Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Yaya zan iya san banda shakka cewa kana da rai madawwami kuma da cewa zaka je sama sa’anda ka mutu?
© Copyright Got Questions Ministries