Tambaya
Yaya zan karɓi gafara daga wurin Allah?
Amsa
Ayyukan Manzanni 13:38 ta ce, “Saboda haka, ƴan’uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.”
Mecece gafara kuma me yasa nake bukatarta?
Kalmar “gafara” ma’ana a goge allo tas, a yafe, a soke bashi. Idan muka yi wani laifi, mukan nemi gafartawa domin a maido da zumunci. Ba’a bayar da gafara domin mutumin ya cancanci a gafarta masa ba. Bubu wanda ya cancanta ayi masa gafara. Gafara aikin ƙauna ce, jinƙai, da alheri. Gafara ta zama a yanke shawara kada a riƙe wata abu gaba da wani mutum, duk da ko menene da suka yi maka.
Littafi Mai Tsarki tana gaya mana cewa dukanmu muna bukatar gafara daga wurin Allah. Dukanmu mun aikata zunubi. Mai Hadishi 7:20 yana shela, “ Ba wani mutum a duniya nan wanda ke aikata abin da ke daidai dukan lokaci, ba tare da yin kuskure ba.” 1Yahaya 1:8 tana cewa, “ In mun ce bamu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuma bata tare da mu.” Dukan zunubi a ƙarshe ya zama yin tawaye ne ga Allah ( Zabura 51:4). A sakamakon haka, muna bukatar gafara da ruwa a jallo. Idan zunubanmu basu sami gafartawa ba, zamu zauna har abada da wahalar sanadiyyar zunubanmu (Matiyu 25:46; Yahaya 3:36).
Gafara- Yaya zan same ta?
Abin godiya, Allah mai ƙauna da jinƙai ne- yana alla-alla ya gafarta mana zunubanmu! 2 Bitrus 3:9 tana cewa, “… amma mai haƙuri gareku, baya so kowa ya halaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.” Allah na da marmari yayi mana gafara, haka nan ne yayi tanadi don gafararmu.
Hukunci kaɗai madaidaici don zunubanmu ita ce mutuwa. Rabin farko na Romawa 6:23 tana shaida, “ Gama sakamakon zunubi mutuwa ne …” Mutuwa na har abada ita ce ladan aiki don zunubanmu. Allah, cikin cikakken shirinsa, ya zama ɗan adam- Yesu Kiristi (Yahaya 1:1,14). Yesu ya mutu kan gicciye, ya ɗauki hukuncin daya cancance mu- mutuwa. 2 Korantiyawa 5:21 tana koya mana, “Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai dashi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.” Yesu ya mutu kan gicciye, ya ɗauke hukuncin da ya cancance mu! A matsayin Allah, mutuwar Yesu ta tanadi gafara don zunuban dukan duniya. 1 Yahaya 2:2 tana shela, “ Shi kansa kuwa shine hadayar sulhu saboda gafarta zunubanmu, ba kuwa namu kaɗai ba, har ma na duniya duka.” Yesu ya tashi daga matattu, yana shelar nasararsa akan zunubi da mutuwa (1 Korantiyawa 15:1-28). Alhamdu lillahi, albarkacin mutuwa da tashin Yesu Kiristi, rabi na biyu na Romawa 6:23 ta zama gaskiya, “…amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.”
Kana son a gafarta maka zunubanka? Kana ji da motsin rai na mai laifi wanda ba zaka iya da alama ka je ka bar ta daga nan? Gafarar zunubanka tana samuwa idan zaka sa bangaskiyarka cikin Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka. Afisawa 1:7 tana cewa, “ Ta gare shi ne muka samu fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah.” Yesu ya biya mana bashinmu, don a iya gafarta mana. Duk abin da zaka yi shine ka tambaye Allah ya gafarta maka ta wurin Yesu, kana gaskatawa cewa Yesu ya mutu da ya biya don gafararka -kuma shi zai gafarce ka! Yahaya 3:16-17 tana ƙunshe da wannan saƙo mai ban mamaki, “ Saboda ƙaunar da Allah yayi wa duniya har ya bada makaɗaici Ɗansa , domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami. Gama Allah bai aiko Ɗansa duniya ya yanke mata hukunci ba, sai dai domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.”
Gafara- da gaske tana da sauƙi haka?
I tana da sauƙi haka! Ba zaka sami ladan aikin gafara daga wurin Allah ba. Ba zaka iya biya don gafartawarka daga wurin Allah ba. Zaka iya kaɗai ka karɓe ta, ta bangaskiya, ta alheri da jinƙan Allah. Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka kuma ka karɓi gafara daga wurin Allah, ga addu’ar da zaka iya yi. Faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto. “Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin daya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alharinka mai ban mamaki da kuma gafara! Amin!”
Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.
English
Yaya zan karɓi gafara daga wurin Allah?