Tambaya
Mece ce shirin ceto?
Amsa
Ko kana jin yunwa? Ba yunwa ta jiki ba, amma kana da yunwa na karin wani abu cikin rayuwa? Akwai wani abu mai zurfi a cikin ka da alamar bai taba samun biyan muradi ba? Idan haka ne, Yesu shine hanya! Yesu ya ce,” Ni ne Gurasa mai bada rai. Wanda yazo gare ni ba zai ji yunwa ba har abada, wanda kuma ya gaskata dani ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada” (Yahaya 6:35).
Ko ka birkita? Ba zaka iya da alama taɓa gano wata turba ko manufa cikin rayuwa? Ko da alama kamar wani ya kakkashe wuta kuma ba zaka iya samo abin kunnawa? Idan haka ne, Yesu shine hanya! Yesu yayi shela”Ni ne Hasken duniya. Wanda ke bi na ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma zai sami hasken rai” ( Yahaya 8:12).
Ko ka taɓa ji kamar an ƙulle ka daga rayuwa? Ko ka taɓa jarraba ƙofofi masu yawa sai kawai ka gano cewa abin da ke bayansu fanko ce da rashin ma’ana? Ko kana neman wata mashigi zuwa cikar rai? Idan haka ne, Yesu shine hanya! Yesu yayi shela,”Ni ne ƙofar, kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo,ya kuma yi kiwo” (Yahaya 10:9).
Ko waɗansu mutane kullum suna baka kunya? Dangatakarka ta zama da mara zurfi kuma fanko? Ko da alama kamar kowa na ƙoƙarin ya cuce ka? Idan haka ne, Yesu shine hanya! Yesu ya ce,”Ni ne Makiyayi- Ni ne makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni” ( Yahaya 10:11,14).
Ko kana mamaki abin da zai gudana bayan wannan rai? Ko ka gaji da yi ƙokwanto wani sa’i ko da rayuwa tana da wata ma’ana? Kana son ka rayu bayan ka mutu? Idan haka ne, Yesu shine hanya! Yesu yayi shela,”Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata dani, ko ya mutu zai rayu . Wanda kuwa ke raye, yake kuma gaskatawa dani, ba zai mutu ba har abada” (Yahaya 11:25-26).
Mece ce hanyar? Mece ce gaskiyar? Mece ce ran? Yesu ya amsa,”Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yahaya 14:6).
Yunwar da kake ji shine yunwar ruhaniya, kuma Yesu ne kaɗai ke iya ƙosarwa. Yesu shine kaɗai wanda zai tada duhu. Yesu shine ƙofar zuwa biyan bukatar rayuwa. Yesu shine aboki da makiyayi wanda kake ta neman sa. Yesu shine rai – a cikin wannan duniya da kuma nan gaba. Yesu ne hanyar ceto!
Dalilin da yasa kana jin yunwa, dalilin da yasa da alama ka ɓace cikin duhu, dalilin da yasa ba zaka iya sami ma’ana cikin rayuwa, shine cewa ka rabu daga Allah. ( Mai Hadishi 7:20; Romawa 3:23). Ramin da kake ji a cikin zuciyarka shine ɓacewar Allah a rayuwarka. An halicce mu da mu zama da dangataka da Allah. Domin zunubanmu, an raba mu daga wannan dangatakar. Har mafi rashin kyau ma, zunubanmu zasu sa mu rabu da Allah har abadan abadin, a wannan rai kuma da nan gaba ( Romawa 6:23; Yahaya 3;36).
Yaya za a iya warware wannan al’amarin? Yesu shine hanya! Yesu ya ɗauki zunubanmu akan sa (2 Korantiyawa 5:21). Yesu ya mutu a madadinmu (Romawa 5;8), ɗauke da hukuncin da ya kamance mu. Kwana uku daga baya, Yesu ya tashi daga matattu, yana gwada nasararsa a bisan zunubi da mutuwa ( Romawa 6:4-5). Me yasa haka ɗin? Yesu ya amsa wancan tambaya da kansa, Ba ƙaunar da tafi haka ga mutane, wato mutum ya bada ransa saboda aminansa” ( Yahaya 15: 13). Yesu ya mutu don mu iya rayu. Idan muka sa bangaskiyarmu cikin Yesu, muna amincewa da mutuwarsa a matsayin biya ne don zunubanmu- dukkan zunubanmu an gafarta kuma an wanke sarai. Sa’anan ne za a ƙosar da yunwarmu na ruhaniya. Za a sake kukkuna wuta. Zamu sami hanya zuwa cikakken rai . Zamu san abokinmu na gaskiya mafi kyau dukka da makiyayi mai kyau. Zamu san da cewa zamu sami rai bayan mu mutu – rai wanda aka tasar daga matattu cikin sama na har abada tare da Yesu!
“Saboda ƙaunar da Allah yayi wa duniya har ya bada makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami” (Yahaya 3:16).
Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.
English
Mece ce shirin ceto?