settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da jima’i kafin aure/kafin aure ayi jima’i?

Amsa


Tare da duk sauran ire-iren fasiƙanci, jima’i kafin aure/kafin aure ayi jima’i yana a hukunce akai akai cikin Littafi (Ayyukan Manzanni 15:20;Romawa 1:29;1Korantiyawa 5;1; 6:13,18; 7:2;10:8; 2Korantiyawa 12:21; Galatiyawa 5:19; Afisawa 5:3; Kolosiyawa 3:5; 1Tasalonikawa 4:3; Yahuza 7). Littafi Mai Tsarki na ɗaukaka ƙaurace wa jima’i kafin aure. Jima’i kafin aure ya zama ba daidai ba ne kamar zina da sauran siffofi na fasiƙanci, saboda dukkansu sun jiɓinci yin jima’i tare da wani da ba aure kuka yi ba. Jima’i tsakanin miji da matarsa ita ce kaɗai irin tarawar da Allah yayi na’am (Ibraniyawa 13:4).

Jima’i kafin aure ya zamanto gama-gari don dalilai da dama. A kullum muna zura ido kan jima’i a ɓangaren “yin wasa” ba tare da yarda da ɓangaren “sake halitta” ba. I, jima’i tana da jin daɗi. Allah ne ya tsara ta wannan hanya. Yana son maza da mata su ji daɗin yin jima’i (cikin iyakaci na aure). Duk da haka, maƙasudin farko na jima’i ba na jin daɗi ba, amma dai na hayayyafa ne. Allah bai hana mana jima’i kafin aure ya ƙwace mana jin daɗi ba, amma ya ƙare mu daga juna biyu da ba a so da yaran da an haifa ga iyaye waɗanda basa son su ko basu shirya domin su ba. Yi zato yadda kyan duniyarmu zata zama idan an bi shirin Allah don jima’i: Cututtukar da kan aikawa ta jima’i zasu ɗan ragu, uwaye marasa aure zasu ɗan ragu, juna biyu da ba a so zasu ɗan ragu, zub da ciki zai ɗan ragu, da sauransu. Ƙauracewa ce kaɗai hanyar Allah in aka zo ga jima’i kafin aure. Ƙauracewa na ceton rayuka, na kariyar jarirai, na bai wa dangantakar tarawa daraja mai dacewa, da kuma mafi muhimmanci dukka na ɗaukaka Allah.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da jima’i kafin aure/kafin aure ayi jima’i?
© Copyright Got Questions Ministries