Tambaya
Allah hakika ne? Yaya zan iya sani da tabbas cewa Allah hakika ne?
Amsa
Mu san Allah hakika ne domin ya bayyana kan sa gare mu cikin hanyoyi uku: cikin halitta, cikin maganar Sa, da cikin Ɗan sa, Yesu Kiristi.
Tabbatarwa mafi tushe na kasancewar Allah shine a saukake abin da shi yayi “Gama tun daga halittar duniya al’amuran Allah marasa ganuwa, wato ikon sa madawwami, da allahntakar sa, sun fahintu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane (marasa bi) sun rasa hanzari” (Romawa 1:20). “Dubi yadda sararin sama ke bayyana daukakar Allah! Dubi yadda suke bayyana a fili ayyuakn sa da yayi! (Zabura 19:1). Idan na samo agogon hannu a tsakiyar wata filin Allah, ba zan ɗauka cewa ta fito ne daga koina ko cewa ta kasance ne kullum ba. Bisa ga tsrin agogon, zan ɗuaka tana da mai shirya ta. Amma na ga da nesa babban tsari kuma takamaimai cikin duniya kewaye damu. Gwajin mu na lokaci bai dogara kan agogai na hannu ba, amma kan hannuwan Allah – juyawar duniya na yau da kullum ( da mallakin tsirkiya na Cesium-133 ƙwayyar zara). Duniya da sammai suna nuna babbar tsari, kuma wannan na jayayya na mai Tsari Babba.
Idan na samo saƙo ta hanyar rubutun asiri, zan nemi mai warwarewa ya taimaka da fashe tsarin rubutun. Zato na zai zama cewa akwai mai fasaha da ya aikar da saƙon, wani wanda ya halicci tsarin rubutun asirin. Yaya wuyar “tsarin rubutun asiri” na DNA da muke ɗauke cikin kowace dan ƙanƙanen ƙwai na naman jikin mu? Ba dai mawuyaci da manufar DNA tana tabbatar da Marubuci Mai Fasaha na rubutun asiri?
Ba kaɗai Allah yayi wata harhaɗe da launi mai kyau na halittar duniya ba, Shi kuma ya girka wata azancin Lahira cikin zuciyar kowane mutum (Mai Hadishi 3:11). Ɗan adam yana da wata fahinta na ciki ciki da cewa rai tana da abin da ke akwai fiye da abin da ido ke gani, cewa akwai wata kasancewa mai tsawo fiye da al’adar duniya na yau da kullum. Azancin mu na lahira tana bayyana kanta a ƙalla cikin hanyoyi biyu: Yin dokoki da sujada.
Kowace wayewar kai na dukkanin tarihi da darajan ta waɗansu dokokin halayen kirki, waɗanda da mamaki sun yi kama daga al’ada zuwa al’ada. Alal misali, aƙidar ƙauna ta zama abin girmamawa na koina a duniya, amma dai yin ƙarya an hukunta koina a duniya. Wannan hali kirki na gama-gari –wannan fahinta na abin da ke daidai da ba daidai ba koina a duniya- tana nuni ga Tarihi Mafi Dukka mai halin kirki wanda ya bamu irin waɗannan tunani.
A hanya iri ɗaya, mutane koina a duniya, ban da kula da al’ada, kullum suna nome hanyar yin sujada. Abin yiwa sujada mai yiwuwa ya bambanta, amma azancin “iko mafi tsauri” ta zama wata sashen ɗan adam wanda ba za a musunta ba. Abin da ke sa mu so yin sujada tana daidai da babu shakka cewa Allah ne ya halicce mu “ cikin siffar sa” (Farawa 1:27).
Allah kuma ya bayyana kansa gare mu ta wurin Maganar sa, Littafi Mai Tsarki. Koina cikin Littafi Mai Tsarki, an ganar da kasancewar Allah a matsayin gaskiyar shaidar kansa (Farawa 1:1; Fitowa 3:14). Sa’anda Benjamin Franklin ya rubuta tarihin kansa, bai ɓata lokaci yi ƙoƙari ya tabbatar da kasancewar kansa ba. Kazalika, Allah ba kashe yawan lokaci tabbatar da kasancewar sa cikin Littafin sa ba. Halin canza rayuwa na Littafi Mai Tsarki, mutuncin ta, da kuma al’ajabai waɗanda suka biyo bayan rubutun ta zasu isa bada garanti na ganin kurkusa.
Hanya na uku wanda Allah ya bayyana kan sa shine ta wurin Ɗan sa, Yesu Kiristi (Yahaya 14:6-11). “Tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake. Kalman nan kuwa Allah ne... Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna cikin mu” (Yahaya 1:1, 14). A cikin Yesu Kiristi “ne cikin jiki dukkan cikar allahntaka ke tabbata” (Kolosiyawa 2:9).
A cikin rayuwar Yesu mai ban mamaki, Ya kiyaye dukkan dokar Tsohon Alkawari kamalalle da cikar annabtai game da Mahadi (Matiyu 5:17). Ya aikata ayyukan jinƙai marar lissaftuwa da al’ajabai a fili na ingantar da sakon sa da kuma bada shaida ga Allahntakar sa (Yahaya 21:24-25). Sa’anan, kwana uku bayan gicciyewar sa, Ya tashi daga matattu, tabbataccen gaskiya daga ɗarurrukan shaidun ido (1Korantiyawa 15:6). Rubutaccen tarihi sun yalwata da “tabbaci” na wane ne Yesu yake. Kanda Manzo Bulus ya faɗa, “don wannan abu ba a ɓoye aka yi shi ba” (Ayyukan Manzanni 26:26).
Mun ankara cewa za a zama kullum da masu shakka waɗanda suna da ra’ayin kan su game da Allah da kuma zasu karanta shaida ta haka ɗin. Kuma za a yi waɗansu waɗanda babu wata jimla na jarrabwa da zai tabbata (Zabura 14:1). Duk takan zo ne ta bangaskiya (Ibraniyawa 11:6).
English
Allah hakika ne? Yaya zan iya sani da tabbas cewa Allah hakika ne?