Tambaya
An sami rai madawwami?
Amsa
Littafi Mai Tsarki ta bayar da tafarki a zahiri zuwa rai madawwami. Da farko, dole ne mu gane cewa mun aikata zunubi gaba da Allah. “Gama ƴan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah” (Romawa 3:23). Dukanmu mun aikata abubuwan da basu gamshi Allah ba, wanda yasa mun cancanci hukunci. Tun da yake duk zunubanmu a ƙarshe gaba da Allah madawwami ne, sai dai hukunci madawwamiya ce ta isa. “Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu” (Romawa 6:23).
Duk da haka dai, Yesu Kiristi, marar zunubi (1 Bitrus 2:22), madawwamin Ɗan Allah ya zama mutum (Yahaya 1:1, 14) kuma ya mutu da ya biya hukuncinmu. “Amma kuwa Allah na tabbatar mana da ƙaunar da yake mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu” (Romawa 5:8). Yesu Kirsti ya mutu akan gicciye (Yahaya 19:31-42), ya ɗauki hukuncin da ya cancance mu (2 Korantiyawa 5:21). Kwana uku daga baya ya tashi daga matattu (1 Korantiyawa 1-4), tabbatarwar nasararsa akan zunubi da mutuwa. “… Wanda ta wurin tsanani jinƙansa ya sake haifarmu, domin muyi rayayyiyar sa zuciya, albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu” (1Bitrus 1:3).
Ta bangaskiya, dole ne mu juyo daga zunubanmu kuma mu juya ga Kiristi don ceto (Ayyukan Manzanni 3:19). Idan muka sa bangaskiyarmu a cikinsa, muka amince ga mutuwar sa akan giccye don biyar zunubanmu, za’a gafarta mana da yi mana alƙawarin rai madawwami cikin sama. “Saboda ƙaunar da Allah yayi wa duniya har ya bada makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami” (Yahaya 3:16). “Wato in kai da bakinka ka bayana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, zaka sami ceto” (Romawa 10:9). Bangaskiya ce kaɗai a cikin aikin Kiristi da ya gama a bisa gicciye ne ta zama hanyar gaskiya tak zuwa rai madawwami! “Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku ba ne, baiwa ce ta Allah, ba kuwa saboda aikin lada ba, kada wani yayi fariya” (Afisawa 2:8, 9).
Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto. “Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”
Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.
English
An sami rai madawwami?