Tambaya
Me ya sa Allah ya zaɓi Isra'ila ta zama zaɓaɓɓun mutanensa?
Amsa
Da yake magana game da jama'ar Isra'ila, Kubawar Shari'a 7:7-9 ya gaya mana, "Ubangiji ya ƙaunace ku, ya zaɓe ku, ba don kun fi sauran al'ummai yawa ba, gama ku ne mafiya ƙanƙanta cikin dukan al'ummai. Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar. Domin haka sai ku sani Ubangiji Allahnku shi ne Allah, Allah mai aminci, mai cika alkawari, mai nuna ƙauna ga dubban tsararraki waɗanda suke ƙaunarsa, suna kuma kiyaye umarnansa."
Allah ya zaɓi al'ummar Isra'ila ta zama mutanen da za a haife Yesu Almasihu - Mai Ceto daga zunubi da mutuwa (Yahaya 3:16). Allah ya fara yiwa Almasihu alkawali bayan faɗuwar Adamu da Hauwa'u cikin zunubi (Farawa sura 3). Daga baya Allah ya tabbatar da cewa Almasihu zai fito daga zuriyar Ibrahim, Ishaku, da Yakubu (Farawa 12:1-3). Yesu Almasihu shine babban dalilin da yasa Allah ya zaɓi Isra’ila ta zama mutanensa na musamman. Allah bai bukaci samun zaɓaɓɓun mutane ba, amma ya yanke shawarar yin hakan ta wannan hanyar. Dole ne Yesu ya fito daga wata al'umma ta mutane, kuma Allah ya zaɓi Isra'ila.
Koyaya, dalilin Allah na zaɓan al'ummar Isra'ila ba don manufar samar da Almasihu ba ne kawai. Burin Allah ga Isra'ila shine su je su koya wa wasu game da Shi. Isra'ila ta kasance ƙasar firistoci, annabawa, da masu mishan zuwa duniya. Nufin Allah shine Isra’ila ta zama mutane na musamman, al’ummar da ke nuna wasu ga Allah da kuma alkawarin da yayi na Mai Fansa, Almasihu, da Mai Ceto. A mafi yawancin, Isra'ila ta kasa wannan aikin. Koyaya, ainihin nufin Allah ga Isra'ila - na kawo Almasihu cikin duniya - ya cika daidai a jikin Yesu Kiristi.
English
Me ya sa Allah ya zaɓi Isra'ila ta zama zaɓaɓɓun mutanensa?