settings icon
share icon
Tambaya

Ko Littafi Mai Tsarki ta koyar da Allahntakar Kiristi?

Amsa


Bugu da ƙari da takamaimai da’awar Yesu game da Kansa, almajiran sa kuma sun yarda da Allahntakar Kiristi. Suna da’awar cewa Yana da iko ya gafarta zunubai – abin da Allah kaɗai ne kan iya yi, tun da yake Allah ne wanda aka yi masa laifin (Ayyukan Manzanni 5:31; Kolosiyawa 3:13; kwatanta Zabura 130:4; Irmiya 31:34). Kusa da alaka da wannan da’awa na karshe, Yesu ne kuma aka ce shine “wanda zai yi wa rayayyu da matattu shari’a” (2Timoti 4:1). Toma ya kira ga Yesu “Ya Ubangijina Allahna kuma” (Yahaya 20:28). Bulus ya kira Yesu “Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu” (Titus 2:13), kuma ya nuna cewa kafin zuwan sa cikin tsoka Yesu ya kasance cikin “Kamannin Allah” (Filibiyawa 2:5-8). Marubucin littafin Ibraniyawa yayi faɗi game da Yesu cewa, “kursiyin ka, ya Allah, na har abada abadin ne” (Ibraniyawa 1:8). Yahaya ya furta cewa , “Tun fil azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman (Yesu) nan kuwa Allah ne” (Yahaya 1:1). Misalan nassoshi sun koyar cewa Allahntakar Kiristi zai iya yawaita (dubi Wahayin Yahaya 1:17; 2:8; 22:13; 1Korantiyawa 10;4; 1Bitrus 2:6-8; kwatanta Zabura 18:2; 95:1; 1Bitrus 5:4; Ibraniyawa 13:20), amma ko ɗayan waɗannan ma ta isa nuna cewa Kiristi an kalle shi da zaman Allah daga mabiyin sa.

An bai wa Yesu kuma sunaye da suke na kaɗai ga Yahweh (sunan Allah daidai bisa doka) cikin Tsohon Alkawari. Sunan Tsohon Alkawari “Mai Fansa” (Zabura 130:7; Yusha’u 13:14) anyi amfani da ita ga Yesu cikin Sabon Alkawari (Titus 2:13; Wahayin Yahaya 5:9). An kira Yesu Immanuwel (“ Allah tare da mu” cikin Matiyu 1). A cikin Zakariya 12:10, Yahweh ne wanda yake cewa, “Zasu dubi wanda suka soke shi” Amma Sabon Alkawari ta shafa wannan ga gicciyewar Yesu (Yahaya 19:37; Wahayin Yahaya 1:7). Idan Yahweh wanda aka soke shi da ana dubawa, kuma Yesu ne wanda aka soke shi da ana dubawa, sa’anan Yesu shine Yahweh. Bulus ya fassarta Ishaya 45:22-23 da shafan Yesu cikin Filibiyawa 2:10-11. Gaba kuma, sunan Yesu ana amfani tare da Yahweh cikin adu’a “Alherin da salama na Allah Uba su tabbata a gareku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu “ (Galatiyawa 1:3; Afisawa 1:2). Da wannan ya zama saɓo idan Kiristi ba Allah bane. Sunan Yesu ya bayyana tare da na Yahweh cikin umarnin Yesu a yi baftisma “da sunan (mufuradi) Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki” (Matiyu 28:19; dubi kuma 2 Korantiyawa 13:14).

Ayyukan da kaɗai Allah ke iya yinsu an danka wa Yesu amanansu. Yesu ba kaɗai ya tada matattu ba (Yahaya 5:21; 11:38-44), da gafarar zunubai (Ayyukan Manzanni 5:31; 13:38), Ya halicce kuma yana riƙe da duniya da sammai (Yahaya 1:2; Kolosiyawa 1:16-17)! Anyi wannan magana ma da dan ƙarfi sa’anda wani ya lura cewa Yahweh ya faɗa Shi kaɗai ne yana nan a loton halitta (Ishaya 44:24). Gaba kuma, Kiristi ya mallaki halayen da Allahntaka kaɗai ke iya samuwa: Madawwami (Yahaya 8:58), kasancewa koina (Matiyu 18:20; 28:20), masanin kome (Matiyu 16:21), mai iko dukka (Yahaya 11:38-44).

Yanzu, abu ɗaya ne ayi da’awar zaman Allah ko a mai da wani wawa ga bada gaskiya abin gaskiya ne, ko dai wani abu kacokan da tabbatar haka yake. Yesu ya miƙa da tabbatarwa al’ajibai da yawa na da’awar Allahntakar sa kuma har ya tashi daga matattu. Kadan kawai na al’ajiban Yesu sun ƙunshi juya ruwa zuwa giya (Yahaya 2:7), warkad da makaho (Yahaya 9:7), gurgu (Markus 2:3), da masu ciwo (Matiyu 9:35; Markus 1:40-42),kuma har da tada mutane daga matattu (Yahaya 11:43-44; Luka 7:11-15; Markus 5:35). Kuma, Yesu kansa ya tashi daga matattu. Nesa daga almaran allolin matsafa da cewa sun mutu sun tashi, babu wata da’awa mai yawan tabbatattun shaida a wajen Littafi Mai Tsarki. Bisa ga Dr. Gary Habermas, akwai aƙalla tabatattun abubuwa na tarihi goma sha biyu da har ma masana masu suka marasa bada gaskiya suka yarda.

1. Yesu ya mutu ta gicciyewa.
2. An binne shi.
3. Mutuwarsa ta sa almajirai fid da zuciya da bege.
4. An gano kabarin Yesu (ko ana da’awa an gano) da zama wofi bayan ƴan kwanaki.
5. Almajirai sun gaskata sun ga bayyanuwar Yesu bayan tashi daga matattu.
6. Bayan wannan almajirai sun sake daga masu shakka zuwa ga masu bada gaskiya da ƙarfin zuciya.
7. Wannan saƙo ita ce cibiyar huɗuba a cikin Ikilisiyar farko.
8. Anyi wa’azin wannan saƙo cikin Urushalima.
9. A sakamakon wannan wa’azi, an haifi Ikilisiya kuma tayi girma.
10. Ranar tashin matattu, Lahadi, ta cika gurbin Assabar a matsayin farko ta ranar sujada
11. Yakubu, mai ƙokwanto, ya tuba sa’anda ya gaskata cewa ya ga Yesu bayan tashi daga matattu.
12. Bulus,abokin gaban Kiristanci, ya tuba ta wurin ji da gani wanda ya gaskata ya zama bayyanuwar Yesu da ya tashi daga matattu.

Ko da idan wani zai ƙi yarda da wannan tsarin dalilai ɗin, kaɗan ne kaɗai da ake bukata a tabbatar da tashi daga matattu kuma a gindaya bishara: mutuwar Yesu, binnewa, tashi daga matattu, kuma da bayyanuwa (1Korantiyawa 15:1-5). Yayin da akwai waɗansu ra’ayoyin da za a bayyana da bada lissafinsu dukka. Masu suka sun yarda cewa almajirai sun yi da’awa sun ga Yesu bayan tashi daga matattu. Babu ƙarairai ko abin da an ɗauka an gani ko ji da zai sauya mutane ta hanyar da tashin matattu yayi. Babu wata bayyani mafi da a ce tashin matattu ga almajirai ne yasa su so mutuwar azaba don imanin su. I, mutane da dama sun mutu don ƙarairai da sun ɗauka sun zama gaskiya, amma babu wani mai mutuwa ga abin da sun sani ya zama ba gaskiya ba.

A ƙarshe dai; Kiristi yayi da’awa shine Yahweh, shi Allah ne (ba kawai “wata allah” ba- amma Allah na Gaskiya), mabiyan sa (Yahudawa da kamata sun razana na bautar gumaka) sun gaaskata Shi kuma sun yi magana gare shi a matsayin haka. Kiristi ya tabbatar da da’awar Allahntakarsa ta wurin al’ajabai ƙunshe da tashin matattu mai canza duniya. Babu wata ra’ayin tunani mai iya bayyana waɗannan tabbatattun abubuwa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Littafi Mai Tsarki ta koyar da Allahntakar Kiristi?
© Copyright Got Questions Ministries