settings icon
share icon
Tambaya

Ko sai Kiristoci sun yi biyayya da dokar Tsohon Alkawari?

Amsa


Mabuɗi game da wannan fito shine sanin cewa dokar Tsohon Alkawari an bayar ne ga al’ummar Isra’ila, ba Kiristoci ba. Waɗansu daga dokokin domin su sa Isra’ilawa sani yadda za a yi biyayya da a gamshi Allah (Alal misali, Dokoki Goma), waɗansun su domin su nuna masu yadda za a yi wa Allah sujada (tsarin hadaya), waɗansu dai a sauƙaƙe domin su mai da Isra’ilawa dabam da waɗansu al’ummomi (sharuɗan abinci da sutura). Babu wata dokar Tsohon Alkawarin da ta shafe mu a yau ba. Sa’anda Yesu ya mutu kan gicciye, Ya kawo ga karshen dokar Tsohon Alkawari (Romawa 10:4; Galatiyawa 3:23-25; Afisawa 2:15).

A madadin dokar Tsohon Alkawari, muna karkashin dokar Kiristi (Galatiyawa 6:2) wanda shine “ Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka. Wannan shine babban doka umarni na farko.umarni nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya” (Matiyu 22:37-40). Idan muka yi wadannan abubuwa biyu, muna cika duk abin da Yesu yana son muyi, “Domin kaunar Allah ita ce mubi umarninsa, umarninsa kuwa ba matsananta ba ne” 1Yahaya 5:2). A kebance, Dokoki Goma ba su ma shafe mu Kiristoci ba. Duk da haka, 9 daga Dokoki Goma an sake maimaita su cikin Sabon Alkawari (duka sai dai dokar a kiyaye Ranar Assabar). Alhali kuwa, idan muna kaunar Allah ba zamu bauta wa wadansu alloli ba ko sujada ga gumakai. Idan muna kaunar makwabtan mu, ba zamu kashe su ba, yi masa karya, yin zina gaba dasu, ko yin kyashin abin da nasu ba. Haka dai, ba na karkashin wata ‘ka’dodin dokar Tsohon Alkawari ba. Mu sai mu kaunaci Allah da kuma kaunaci makwabatan mu. Idan mun yi wadancan abubuwa biyu da aminci, kome dai zai yi daidai.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko sai Kiristoci sun yi biyayya da dokar Tsohon Alkawari?
© Copyright Got Questions Ministries