settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne abin nufi da a maya haifuwar Kirista?

Amsa


Mene ne abin nufi da a maya haifuwar Kirista? Daɗaɗɗen maganar da aka tsinto daga Littafi Mai Tsarki wanda ta bada amsar wannan tambaya ita ce Yahaya 3:1-21. Ubangiji Yesu Kiristi yana zance da Nikodimu, mashahurin Bafarisiye kuma memba na Sanhedrin (wani basaraucen Yahudawa). Nikodimu yazo wurin Yesu daddare. Nikodimu yana da tambayayoyi yayi wa Yesu.

Da Yesu yana Magana tare da Nikodimu, Ya ce, “… Lalle hakika ina gaya maka, in ba a sake haifar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba.” Nikodimu ya ce masa, ” ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato ya iya komawa cikin uwa tasa ta sake haifo shi?” Yesu ya amsa, “ lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da ta kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga mulkin Allah ba. Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin da kuma Ruhu ya haifa ruhu ne. Kada kayi mamaki don nace maka, ‘Dole ne a sake haifarka’…” (Yahaya 3:3-7)

Jimlar “ maya haifuwa” a zahiri tana nufin “haifuwa daga sama.” Nikodimu yana da bukata na ainihi. Ya bukace canji na zuciyarsa …sakewa ta ruhaniya. Sabuwar haifuwa, a sake haifuwa, ya zama aikin Allah ne ta yadda akan ba mutumin da ya gaskata rai madawwami (2 Korantiyawa 5:17; Titus 3:5; 1Bitrus 1:3; 1Yahaya 2:29; 3:9; 4:7; 5:1-4,18). Yahaya 1:12,13 tana nuna cewa, “maya haifuwa” kuwa tana ɗauke da ra’ayi “a zama ƴaƴan Allah” ta wurin amincewa cikin sunan Kiristi.

Azancin tambaya ta zo ne, “Me yasa mutum yana bukatar maya haifuwa?” manzo Bulus cikin Afisawa 2:1 yana cewa, “Ku kuma ya raya ku sa’ada kuke matattu ta laifofinku da zunubanku…” Ga mutanen Romawa cikin Romawa 3:23, Manzon ya rubuta, “Gama ƴan adam duka sunyi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.” Hakanan, mutum na bukatar maya haifuwa domin a gafarta zunubansu kuma a sami dangataka da Allah.

Yaya haka zai zo ya faru? Afisawa 2:8.9 ta bayyana, “ Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku bane, baiwa ce ta Allah, ba kuwa saboda aikin lada ba, kada wani yayi fariya.” Yayin da aka “cece” wani, an riga maya haifuwarsa/ta, sabuntawar ruhaniya, kuma yanzu ya zama ɗan Allah ta hakkin sabuwar haifuwa. Amincewa cikin Yesu Kiristi, Shi wanda ya biya hukuncin zunubi lokacin da Ya mutu akan gicciye, shine abin da ake nufin da “maya haifuwa” a ruhaniya. “Saboda haka, duk wanda ke na Almasihu, sabuwar halitta ne , …” (2 Korantiyawa 5:17).

Idan baka taɓa amincewa cikin Ubangiji Yesu Kirsti a matsayin mai cetonka ba, ko zaka yi tunanin kutawar Ruhu Mai Tsarki da yake Magana a zuciyarka? Kana bukata a maya haifuwarka ko zaka yi addu’ar tuba kuma ka zama sabuwar halitta cikin Kiristi, yau? “Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa,ya basu ikon zaman ƴaƴan Allah, wato waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga kwaɗayin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah” (Yahaya 1:12-13).

Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto. “Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne abin nufi da a maya haifuwar Kirista?
© Copyright Got Questions Ministries