settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Kiristanci kuma mene ne Kiristoci ke bada gaskiya?

Amsa


1 Korantiyawa 15:1-4 tana cewa, “ Yanzu kuma, ƴan’uwa, zan tuna maku da bisharar da sanar da ku, wadda kuka karɓa, wadda kuke bi, wadda kuma ake ceton ku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku kankan, in ba sama sama ne kuka gaskata ba. Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shine wanda na karɓo, cewa Almasihu ya mutu domin zunuban mu, kamar yadda littattafai suka faɗa, cewa an binne shi, an tada shi a rana ta uku, kamar yadda littattafai suka faɗa.”

A dunƙule dai,wancan shine bangaskiyar Kiristanci. Kiristanci na dabam a cikin dukkan sauran imani, domin Kiristanci tana mafi game da dangantaka ne, da aikatawar addini. Maimakon a manne ga tsarin “yi da kada ayi.” Manufar Kirista shine a nome tafiya ta kurkusa tare da Allah Uba. Wancan dangantaka tana yiwuwa ne don aikin Yesu Kiristi, da aikin Ruhu Mai Tsarki a cikin rayuwar Kirista.

Kiristoci sun bada gaskiya cewa Littafi Mai Tsarki hurarre ne, maganar Allah marar kuskure, kuma cewa koyarwar ta shi ke da ƙarshen iko (2 Timoti 3:16; 2 Bitrus 1;20-21). Kiristoci sun bada gaskiya cikin Allah ɗaya da ya kasance cikin mutum uku, Uba, da Ɗa (Yesu Kiristi), da kuma Ruhu Mai Tsarki.

Kiristoci sun bada gaskiya cewa ɗan adam an halicce shi takamaimai da samun dangantaka da Allah, amma zunubi ya raba dukkan mutane daga Allah (Romawa 5:12; Romawa 3:23). Kiristanci tana koyar cewa Yesu Kiristi yayi tafiya a wannan duniya, Allah cikakke, amma tukuna cikakken mutum (Filibiyawa 2:6-11), kuma ya mutu akan gicciye. Kiristoci sun bada gaskiya cewa bayan mutuwar sa a kan gicciye, an bine Kiristi, Ya tashi kuma, kuma yanzu yana raye a hannun dama na Uba, yana roko domin masu bada gsakiya har abada (Ibraniyawa 7;25). Kiristanci na shela cewa mutuwar Yesu akan gicciye ta isa gaba ɗaya ta biya bashin zunubi da dukkan mutane sun riƙe kuma wannan ne ya maido da ƙaryayyen dangantaka tsakanin Allah da mutum (Ibraniyawa 9:11-14; 10:10; Romawa 6:23; Romawa 5:8).

Garin a sami ceto, dole ne mutum a sauƙaƙe yasa bangaskiyar sa ɗungum a cikin aikin da Kiristi ya gama a kan gicciye. Idan wani ya gaskata cewa Kiristi ya mutu a madadin sa kuma ya biya farashin zunuban sa, kuma ya sake tashi, sa’anan mutumin ya sami ceto.Ba wani abin da wani zai iya yi ya sami ladan ceto. Ba wani da zai zama da “isasshen nagarta” ya gamshi don kan sa ko kan ta, domin dukkan mu masu zunubi ne (Ishaya 64:6-7; Ishaya 53:6). Na biye, ba wani ƙarin abu da za a yi, domin Kiristi yayi dukkan aiki! Yayin da yana kan gicciye, Yesu ya ce, “an gama!” (Yahaya 19:30).

Daidai kamar yadda babu abin da wani zai iya yi ya sami ladan ceto, da zarar wani ya aza amincewar sa/ta cikin aikin Kiristi a kan gicciye, babu abin da wani zai iya yi ya rasa ceton sa/ta kuwa. Tuna, Kiristi yayi aikin kuma ya gama! Ba wani abu game da ceto da ta‘allaƙa ga wanda ya karbe ta! Yahaya 10:27-29 ta furta “ Tumaki nan nawa sukan saurari murya ta, na san su, suna kuma bi na. Ina basu rai madawwami, ba kuwa zasu halaka ba har abada, ba kuma [mutum] mai kwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya bani [su], yafi duka girma, ba kuwa [mutum] mai iya kwace [su] daga ikon Uban.”

Waɗansu zasu yi tunani, “Tubarkalla!...an cece ni kai tsaye, zan iya yi kawai yadda na so, kuma ba zan rasa ceto na ba!” Amma ceto bai game da zaman ƴanci na yin abin da wani ya so ba ne. Ceto shine a zamo da ƴanci daga zaman bautar tsohuwar halin zunubi, kuma a zama ƴantacce a bi daidaitaccen dangantaka da Allah. Muddar masu bi suna rayuwa a wannan duniya cikin jikunan su na zunubi, zai zama koyaushe akwai gwagwarmaya da bada kai ayi zunubi. Rayuwa cikin zunubi yana toshe dangantakar da Allah ke nema ya samu da ɗan adam, ba zai ji daɗin dangantakar da Allah yayi niyya samuwa da shi ba. Duk da haka, Kiristoci zasu iya samun nasara akan fama da zunubi ta nagari da shafan maganar Allah (Littafi Mai Tsarki) cikin rayukan su, da kuma sarrafawar Ruhu Mai Tsarki – wato, miƙa wuya ga tasirin Ruhu da bishewa cikin halin kowace rana, da kuma ta Ruhu ayi biyayya da maganr Allah.

Hakanan, yayin da tsarin addinai masu yawa suna bukatar mutum yayi waɗansu abubuwa ko da yayi waɗansu abubuwa, Kiristanci tana game da samun dangantaka da Allah. Kiristanci na game da gaskatawa cewa Kiristi ya mutu a kan gicciye a matsayin biya na zunubai na kanka da kuma ya tashi. Bashin zunuban ka an biya kuma zaka iya samu zumunci da Allah. Zaka iya sami nasara aka halin zunuban ka da tafiya cikin zumunta da biyayya da Allah. Wannan ne Kiristanci na gaskiya bisa Littafi Mai Tsarki.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Kiristanci kuma mene ne Kiristoci ke bada gaskiya?
© Copyright Got Questions Ministries