settings icon
share icon
Tambaya

Ko Yesu Allah ne? Ko Yesu ya taɓa yin da’awa da zaman Allah?

Amsa


Ba a taɓa rubuta cikin Littafi Mai Tsarki Yesu na faɗi da kalmomi daidai “Nine Allah” ba. Wannan baya nufin, duk da haka, cewa Bai furta Shi ne Allah ba. A ɗauki bisa misali kalmomin Yesu cikin Yahaya 10:30, “Ni da Uba ɗaya muke.” A duban farko, wannan ba mai yiwuwa ne ya zamanto da’awa ba zaman Allah ba ne. Duk da haka, dubi yadda Yahudawa suka ji da furcin sa, “Ba don wani aikin nagari zamu jajjefe ka ba, sai don saɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah” (Yahaya 10:33). Yahudawa sun gane da furcin Yesu da zaman da’awa ya zama Allah. A cikin ayoyi na biye Yesu bai taɓa yin gyara wa Yahudawa ta cewa, “ Ban yi da’awa ni ba Allah ba ne.” Wannan na nuni Yesu da gaske yana cewa Shi Allah ne ta furtawa, “Ni da Uba ɗaya muke” (Yahaya 10:30). Yahaya 5:59 ya zama wata misali. Yesu yayi shela, “ Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!” Har ila yau, cikin amsawa, Yahudawa suka kwashi duwatsu cikin ƙoƙari a jajjefi Yesu (Yahaya 8:59). Me yasa Yahudawa zasu so su jajjefi Yesu idan da bai faɗi wani abin da sun gaskata ya zama saɓo, wato, da’awar zaman Allah?

Yahaya 1:1 tana cewa, “ Kalman nan kuwa Allah ne .” Yahaya 1:14 tana cewa “Kalman nan kuwa ya zama mutum.” Wannan a fili tana nunin cewa Yesu shine Allah cikin tsoka. Ayyukan Manzanni 20:28 tana gaya mana , “... da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuma kiwon Ikilisyar Allah wadda ya samo wa kansa da jinin sa .” wane ne ya sayo Ikilisiya da jinin kansa? Yesu Kiristi. Ayyukan manzanni 20:28 ta furta cewa Allah ya sayo Ikilisiya da jinin kansa. Don haka, Yesu Allah ne!

Toma almajiri ya furta game da Yesu, ‘ Ya Ubangiji na, Allah na kuma!” (Yahaya 20:28). Yesu bai gyara masa magana ba. Titus 2:13 tana ƙarfafa mu mu jira ga dawowar Allahnmu da mai Ceto- Yesu Kiristi (dubi kuma 2Bitrus 1:1). A cikin Ibraniyawa 1:8, Uban ya furta ga Yesu, “ Amma game da Ɗan ya ce, “kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne, sandan sarautarka sanda ne na tsantsar gaskiya.”

A cikin Wahayin Yahaya, Mala’ika ya umarci Manzo Yahaya da yayi wa Allah kaɗai sujada (Wahayin Yahaya 19:10). Sau tari cikin Littafi Yesu ya amshi sujada (Matiyu 2:11; 14:33; 28:9,17; Luka 24:52; Yahaya 9:38). Bai taɓa tsauta wa mutane don yi masa sujada ba. Idan Yesu ba Allah ba ne, da ya gaya wa mutane kar suyi masa sujada ba, daidai yadda mala’ika ya yayi cikin Wahayin Yahaya. Akwai waɗansu ayoyi da dama da maganganun da aka tsinto daga Littafi da suna jayayya don allahntakar Yesu.

Dalili mafi muhimmanci cewa Yesu sai da ya zama Allah shine cewa idan Shi ba Allah bane, mutuwarsa da bata isa ta biya hukunci don zunubai na dukkan duniya ba ( 1Yahaya 2:2). Allah kaɗai ne zai iya biya irin hukunci marar iyaka haka. Allah kaɗai ne zai iya ɗaukar zunuban duniya (2 Korantiyawa 5:21), ya mutu, kuma ya tashi- tabbatarwar nasarararsa akan zunubi da mutuwa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Yesu Allah ne? Ko Yesu ya taɓa yin da’awa da zaman Allah?
© Copyright Got Questions Ministries