Tambaya
Mene ne madaidaicin addini domina?
Amsa
Gidajen abinci mai sauri suna sa mu marmari ta yardar mana muyi odar abincinmu daidai yadda muke son ta. Waɗansu kantunan ruwan kofi suna fariya kan ɗarurrukan ɗanɗano dabam dabam da kuma ire-iren ruwan kofi. Ko ma a yayin sayen gidaje da motoci, mukan iya dubi ɗaya da kuma na dukan ganin dama ta fuskokin da muke sha’awa. Ba ma sauran rayuwa kawai cikin duniyar cakulat, banilla, da strawberry (wani irin ruwan zaki na wata ƴaƴan itace). Zaɓi shine sarki! Zaka iya gano game da kome da kake so bisa ga son ka da bukatun kanka.
Haka nan yaya game da addinin da yake daidai dominmu? Yaya game da addinin da babu alhakin laifi, baya neman hakokki, baya da abin nauyaya da yawan damuwa akan yi ko kada kayi? Yana nan can, daidai yanda nayi kwatance, amma abu ne wanda akan zaɓa kamar ɗanɗanon ruwan ƙanƙara na afarari da aka fi so?
Akwai muryoyi da dama da suke neman kulawarmu, hakanan me yasa wani zai ɗauki Yesu fiye da , a ce, Muhammadu ko Confucius, Buddha, ko CharlesTaze Russell, ko Joseph Smith? Bayan duk, ba dukkan hanyoyi ne suna nufa zuwa sama ba? Ba dukkan addinai ne sun nufa zuwa sama daidai kamar yadda ba dukkan hanyoyi ne suna nufa zuwa Indiana ba.
Yesu kaɗai ne ke magana da iznin Allah domin Yesu kaɗai ne yaci nasara da mutuwa. Muhammadu, Confucius, da dai sauransu suun ruɓe cikin kaburburansu har ya zuwa yau, amma Yesu, da ikon kansa, yayi tafiyar sa can daga kabari kwana uku bayan mutuwa akan azabtaccen gicciyen Romawa. Kowane da ke da iko akan mutuwa ya cancanci kulawarmu. Kowane da ke da iko akan mutuwa ya cancanci saurarawarmu.
Shaida mai ƙarfafa tashin Yesu daga matattu mai nauyi ne. Da farko, akwai shaidun ido fiye da ɗari biyar na tashin Yesu. Waɗannan shaidun ido suna da ɗan dama. Ba za a iya ƙyale muryoyi ɗari biyar ba. Akwai al’amarin fankon kabari; maƙiyan Yesu ba wuya da sun tsayar da duk zancen tashin matattu ta wurin haifar da mataccen, rubabben jikinsa, amma babu wata matacciyar jiki domin su haifar ba! Kabari ta zama fanko! Da almajirai sun iya sace jikinsa? Da kyar. Da a hana wannan faruwa, an maka wa kabarin Yesu tsaro da sojoji masu makamai. Idan an lura mabiyansa mafi kurkusa cikin tsoro sun gudu a yayin kamawa da gicciyewarsa. Ya zama mafi marar yiwuwa ne wannan matsoratan kungiyar masunta yafe da tsummoki da su bi ɗai ɗai gaba da horarru da gogaggun sojoji. Tabbataccen abu mai sauƙi shine cewa tashin Yesu daga matattu ba ta musuntuwa!
Kuma, kowane wanda yake da iko akan mutuwa ya cancanci a saurara. Yesu ya jarraba ikonsa akan mutuwa, don haka, muna bukatar mu ji abin da yana faɗi. Yesu yana da’awa da shine kaɗai hanyar ceto ( Yahaya 14:6). Shi ba wata hanya ba ce; shi ba ɗaya daga cikin hanyoyi masu yawa bane, amma Yesu ne hanya.
Kuma daidai wannan Yesu ya ce,” Ku zo gare ni dukan ku masu wahala, masu fama da kaya, ni kuwa zan hutasshe ku” (Matiyu 11:28). Wannan tattauran duniya da rayuwa mai wuya. Yawancin mu muna jina-jina, je ka huda, da tabban fama. An yarda? Haka mene ne kake so? Gyara ne ko addini kawai? Rayayyen mai ceto ko ɗaya daga matattun”annabawa” masu yawa? Dangataka mai ma’ana ko fankon ibada? Yesu ba zaɓi ba ne--- Shi ne mai kyau.
Yesu ne”addini” na gaskiya idan kana neman gafara (Ayyukan manzanni 10:43). Yesu ne”addini” na sosai idan kana neman dangataka mai ma’ana da Allah (Yahaya 10:10). Yesu ne”addini” na gaskiya idan kana neman madawwamiyar gida cikin sama (Yahaya 3:16). Ka aza bangaskiyar ka cikin Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka – ba zaka ce da na sani ba! Ka amince da shi domin gafarar zunubanka – ba zaka ji cizon yatsa ba.
Idan kana son ka sami”dangataka na gaskiya” tare da Allah, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto.”Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”
Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.
English
Mene ne madaidaicin addini domina?