settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Kirista?

Amsa


Ƙamus na Webster ta bada ma’anar Kirista da kamar”mutum mai sa bangaskiya cikin Yesu a matsayin Kiristi ko cikin addini mai asali akan koyarwar Yesu.” Sa’anda wannan ya zama wurin farawa mai kyau cikin ganewa da abin da Kirista yake, kamar yawancin ma’anonin zaman duniya, ta faɗi gajeruwa kaɗan da ainihin sadarwar Littafi Mai Tsarki na abin da ake nufi da zaman Kirsita.

Kalmar”Kirista” an more shi sau uku cikin Sabon Alƙawari (Ayyukan Manzanni 1:28; 26:28; 1Bitrus 4:16). An ƙira mabiyan Yesu Kiristi da farko”Kiristoci” cikin Antakiya (Ayyukan Manzanni 11:26) domin halaya, ayyuka, da maganarsu kamar da Kiristi ne. Daga tushe mutane marasa ceto ne daga Antakiya suka yi amfani da ita kamar wata irin laƙabin raini domin yi wa Kiristoci dariya. A zahiri tana nufin,”zama dan jam’iyyar Kiristi” ko dai”mai bin ra’ayi ko mabiyin Kiristi,” Wanda shine mai kama ainun da yadda ƙamus na Webster ta bayyana ta.

Da rashin sa’a ana nan dai, kalmar”Kirista” ta ɓatar da babban tasirinta mai yawa kuma kullum ana morarta ga wani wanda yake mai addini ne, ko yana da gawurtaccen halayen kirki maimakon mabiyin Yesu Kiristi da aka maya haifuwarsa da gaske. Mutane da yawa waɗanda basu bada gaskiya da amince cikin Yesu Kiristi ba sun ɗauki kansu Kiristoci ne don kawai suna tafiyar ikilisiya ko suna zama a cikin al’ummar”Kirista.” Amma zuwa ikilisiya, a bauta wa marasa galihu kasa da kai, ko zaman mutumin kirki baya mai da kai Kirista ba. Kamar ɗayan mai bishara ya taɓa faɗi,” zuwan ikilisiya baya maida wani Kirista ba, daidai yadda zuwan tashar mota baya mai da wani mota ba.” Zaman memba na ikilisiya, zuwan sujadai kullum, bayarwa ga aikin ikilisiya baya mai da kai Kirista ba.

Littafi Mai Tsarki tana koyar mana cewa ayyukan masu kyau da muke yi ba zasu iya mai da mu karɓaɓɓu ga Allah ba. Titus 3:5 tana gaya mana cewa” ba wai don wani aikin adalci da muka yi ba, a’a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sake haifuwa, da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki .” Haka nan, Kirista shine wani wanda aka maya haifuwarsa daga Allah (Yahaya 3:3; Yahaya 3:7; 1 Bitrus 1:23), kuma sun sa bangaskiyarsu da amincewa cikin Yesu Kiristi. Afisawa 2:8 tana gaya mana cewa”Domin ta wurin alheri ne aka cece ku saboda bangaskiya, wannan kuwa ba ƙoƙarin kanku bane, baiwa ce ta Allah.” Kirista na gaskiya shine wanda ya tuba daga zunubansa ko zunubanta kuma ya sa bangaskiya da amincewa cikin Yesu Kiristi kadai. Amincewarsa ba ya cikin bin addini ko tsarin dokoki na halin kirki ko dai jerin abubuwan da za a yi da ba za a yi ba.

Kirista na gaskiya shine mutum wanda ya sa bangaskiyarsa ko bangaskiyarta da amince cikin mtuntakar Yesu Kiristi kuma babu shakka cewa ya mutu bisa gicciye a biyarwar zunubai da tashin daga matattu kuma a rana ta uku da ya sami nasara kan mutuwa da kuma bayar da rai madawwami ga duk wanda ya gaskata da shi. Yahaya 1:12 tana gaya mana:” Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato masu gaskatawa da sunansa, ya basu ikon zaman ƴaƴan Allah,” Kirista na gaskiya da gaske ya zama dan Allah, rukunin iyalin Allah na gaskiya, kuma wani ne wanda ya sami sabuwar rai cikin Kiristi. Alamar Kirista na gaskiya shine ƙauna don waɗansu da biyayya ga Maganar Allah ( 1 Yahaya 2:4; Yahaya 2:10).

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Kirista?
© Copyright Got Questions Ministries