settings icon
share icon
Tambaya

Ko akwai rai bayan mutuwa?

Amsa


Ko akwai rai bayan mutuwa? Littafi Mai Tsarki tana gaya mana,” Mutum duka kwanakin ransa gajere ne, kwanakin wahala kuma. Sukan yi girma su bushe nan da nan kamar furanni, sukan shuɗe kamar inuwa... idan mutum ya mutu, zai sake rayuwa kuma?” (Ayuba 14:1-2,14).

Kamar Ayuba, kusan dukanmu mun sani ƙalubale ta wannan tambaya. Daidai mene ne ke faruwa damu bayan mutuwarmu? Ko kawai mu kan daina kasancewa ne? Ko rai kamar kofa ce mai kewaya mai kai da komowa duniya garin a sami wata girma na mutum da kansa? Ko kowa da kowa na zuwa wuri ɗaya, ko dai mukan je wurare dabam dabam? Ko da gaske akwai sama da jahannama, ko dai matsayin tunani ne kawai?

Littafi Mai Tsarki tana gaya mana cewa ba kaɗai akwai rai bayan mutuwa ba, amma rai madawwami mai ɗaukaka da”Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, waɗanda Allah ya tanadar wamasu ƙaunarsa” (1 Korantiyawa 2:9). Yesu Kiristi , Allah cikin tsoka, yazo duniya da ya bamu wannan baiwa na rai madawwami.”Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya ƴantar da mu, dukan da aka yi tayi masa, yasa muka warke” (Ishaya 53:5).

Yesu ya ɗauki hukuncin da kowanen mu ya cancanci kumaya saɗaukar da ainihin ransa. Kwana uku daga baya, ya gwada kansa mai nasara bisa mutuwa ta tashiwa daga kabari, cikin Ruhu da kuma cikin tsoka. Ya saura bisa duniya na kwana arba’in kuma dubbai sun shaide shi kafin tashiwa zuwa madawwamiyar gidansa cikin sama. Romawa 4:25 na cewa,”Wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi domin mu sami kuɓuta ga Allah”

Tashin Kiristi ya zama aukuwar da aka sanya cikin rubutu sosai. Manzo Bulus ya ƙalubalanci mutane da tambayar ingancin shaidun ido, kuma babu wanda ya iya ya hauri gaskiyarta. Tashi daga matattu ne dutsen kusurwa na Bangaskiyar Kirista; don an tashe Kiristi daga matattu, zamu iya zama da bangaskiya cewa, mu ma, za a tashe mu.

Bulus ya ƙarfafa waɗansu Kiristoci na farko waɗanda basu gaskata da wannan,”To, da yake ana wa’azin Almasihu kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansun ku ke cewa babu tashin matattu? In dai babu tashin matattu, ashe, ba a tada Almasihu ba ke nan” (1 Korantiyawa 15:12-13).

Kiristi ne farko kaɗai na babban girbi na waɗanda za a tashe su zuwa rai kuma. Mutuwar jiki ta shigo ta wurin mutum guda, Adamu, ga wanda dukanmu ke da dangataka. Amma duk wanda aka tallafa zuwa iyalin Allah ta bangaskiya cikin Yesu Kiristi za a basu sabuwar rai (1 Korantiyawa 15:20-22). Daidai kanda Allah ya tashe jikin Yesu, haka nan jikunanmu za a tasar a dawowar Yesu (1 Korantiyawa 6:14).

Ko da yake dukanmu a ƙarshe za a tashe mu, ko waɗanne ba zasu je cikin sama tare ba. Dole kowane mutum yayi zaɓi a wannan rai ya ƙuduri inda shi ko ita zai je na har abadan abadin. Littafi Mai Tsarki tana cewa an ƙudurta mana mu mutu sau ɗaya tak, kuma bayan wannan shari’a zai zo (Ibraniyawa 9:27). Waɗannan da aka maishe su masu adalci zasu je zuwa rai madawwami cikin sama, amma marasa bangaskiya za a aikar da su ga madawwamiyar hukunci, ko jahannama ( Matiyu 25:46).

Jahannama, kamar sama, ba matsayin kasancewa ba ce kadai, amma wuri ne na zahiri, kuma na ainihin gaske. Ta zama wuri ne inda marasa adalci zasu ji madawwamyar fushi marar ƙarewa daga Allah. Zasu jure wa azabar sosuwar rai, hankali, da kuma jiki, da sane zasu wahala daga kunya, yi da na sani, da kuma raini.

Ana kwatancin jahannama da kamar rami marar matuƙa (Luka 8:31; Wahayin Yahaya 9:1), da kuma tafkin wuta , mai ƙonewa da farar wuta, inda mazauna zasu sha azaba dare da rana har abada da abadin (Wahayin Yahaya 20:10). A cikin jahannama, za a yi kuka da cizon haƙora, alamar mugun baƙin ciki da hasala (Matiyu 13:42). Ta zama wuri ne” A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta” (Markus 9:48). Allah ba ya jin daɗin mutuwar mugu, amma yana sha’awar su juyo daga miyagun hanyoyi domin su rayu (Ezekiyel 33:11). Amma ba zai tilasta mu ga yin biyayya; idan muka zaɓa mu ƙi karɓarsa, yana da ƙaramin zaɓi amma dai ya bamu abin da muka so- yi zama banda shi.

Rayuwa a duniya ta zama gawaji ne – shiri domin abin da ke zuwa. Ga masu bada gaskiya, wannan shine rai madawwami nan da nan a gaban Allah. Hakanan yaya aka maishe mu masu adalci da kuma iya karɓar wannan rai madawwami? Akwai hanya guda ɗaya kaɗai- ta wurin gaskata da amince cikin Ɗan Allah, Yesu Kiristi. Yesu ya ce ,”Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata dani, ko ya mutu zai rayu . Wanda kuwa ke raye, yake kuma gaskatawa dani, ba zai mutu ba har abada---“ (Yahaya 11:25-26).

Kyautar baiwar rai madawwami tana samuwa ga dukka , amma tana bukatar cewa mu musunci kanmu waɗansu jin daɗin duniya da mu saɗaukar da kanmu ga Allah.”Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gareshi” (Yahaya 3:36). Ba za a bamu damar tuba daga zunubanmu bayan mutuwa ba, domin da dai mun ga Allah fuska da fuska, ba zamu sami wata zaɓi ba amma mu bada gaskiya gareshi. Yana son mu zo wurinsa cikin bangaskiya da ƙauna ga Allah, an lamunce mana ba kaɗai muyi rayuwa mai ma’ana a duniya ba, amma har ma da rai madawwami a gaban Kiristi.

Idan kana son ka karɓi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ga samfurin addu’a anan. Ka tuna, faɗar wace nan addu’a ko wata addu’a dabam ba zai cece ka ba. Amincewa ce kaɗai cikin Kiristi wanda zai iya cece ka daga zunubi. Wace nan addu’a, hanya ce mai sauƙi a furta ga Allah bangaskiyarka a cikin Sa kuma ka gode masa don ya tanadar maka da ceto.”Allah, na sani cewa nayi zunubi gareka kuma na cancanci hukunci. Amma Yesu Kiristi ya ɗauki hukuncin da ya cancance ni, don ta wurin bangaskiya a cikinsa in sami gafartawa. Na juyo daga zunubaina kuma na sa amincewa tawa a cikinka don ceto. Na gode maka don alherinka mai ban mamaki da kuma gafara – kyautar rai madawwami! Amin!”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko akwai rai bayan mutuwa?
© Copyright Got Questions Ministries