settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke koyar game da Triniti?

Amsa


Abu mafi wahala game da tunanin Kirista na Triniti shine cewa ba wata hanya a bayyana ta isasshe. Triniti ta zama tunanin da ba zata yiwu ga wani bani adam ya gane ta cikakke ba, ko ma a bayyana ta. Allah mafi girma da rashin iyaka fiye da mu yake, don haka kada mu tsammaci zamu iya mu gane da shi cikakke, Littafi Mai Tsarki tana koyar cewa Uban Allah ne, cewa Yesu Allah ne, da kuma cewa Ruhu Mai Tsarki Allah ne. Littafi Mai Tsarki ma ta koyar cewa akwai Allah daya tilo kadai. Ko da yake zamu iya gane da wasu abubuwa game da dangantakar dabam dabam na mutanen Triniti ga junansu, a ƙarshe, ba ta fahintuwa ga tunanin mutum. Duk da haka, wannan bai nuna bai zama gaskiya ba ko kuma bai zama kan su koyarwar Littafi Mai Tsarki ba.

Ka riƙe a tunani yayin da kake nazarin wannan fanni cewa kalmar ‘Triniti” ba a more ta cikin l Littafi ba. Wannan sharaɗi ne da aka mora da ƙoƙarin bayyana ukuntakar Allah, batu cewa akwai 3 masu kasancewa tare, mutane dawwamammu sune suka zama Allah. Ka gane cewa wanna BA KO KADAN a kowanne hanya na bada shawara Allahloli 3 ba ne. Triniti ta zama Allah 1 ne wanda yake mutum 3. Babu wani ila da morar kalmar “Triniti” ko da yake kalmar ba a gano ta cikin Littafi Mai Tsarki ba. Yana da gajerta a fadi kalmar “Triniti” da a fadi “3 masu kasancewa tare, dawwamammu mutane suka zama Allah 1.” Tukuna dai, mun san akwai kakkani cikin Littafi Mai Tsarki. Ibrahim ne kakan Yakubu. Kada ka rataya kan kalmar “Triniti” kanta. Abin da ya kamata ya zama ainihi da muhimmanci shine cewa tunanin da ke WAKILCI da kalmar “Triniti” tana nan cikin Littafi. Da muka idar da wannan gabatarwa, za a bayar da ayoyin Littafin Mai Tsarki cikin muhawarar Triniti.

1) Akwai Allah ɗaya tak: Maimaitawar Shari’a 6:4; 1Korantiyawa 8:4; Galatiyawa 3:20; 1Timoti 2:5.

2) Triniti ta ƙunshi mutum uku: Farawa 1:1; 1:26; 3:22; 11:7; Ishaya 6:8; 48:16; 61:1; Matiyu 3:16-17; 28:19; 2Korantiyawa 13:14. A cikin nassoshin Tsohon Alƙawari, sanin Yahudanci na da taimako. Cikin Farawa 1:1, jam’in sun “Elohim” aka mora. Cikin Farawa 1:26; 3:22; 11:7 da kuma Ishaya 6;8, jam’in suna ta “mu” aka mora. Wannan “Elohim” da “mu” na nuna fiye da biyu BANDA tambaya. Cikin Turanci, kana da siffofi biyu kadai, mufuradi da jam’i. Cikin Yahudanci, kana da siffofi uku: mufuradi, na mutum biyu, da kuma jam’i. Na mutum biyu ya zama na biyu ne KAƊAI. Cikin Yahudanci, siffar na mutum biyu ana morarta ga abubuwa da sukan zo ne cikin bibbiyu kamar idanu, kunnuwa, da hannaye. Kalmar “Elohim” da kuma sunan “mu” siffofin jam’i ne – tabbatacce fiye da biyu – kuma dole na nunin uku ko fiye ma (Uba, Ɗa, Ruhu Mai Tsarki). A cikin Ishaya 48:16 da 61:1, Ɗan yana magana yayin da yana batu ga Uban da kuma Ruhu Mai Tsarki. Kwatanta Ishaya 61:1 da Luka 4:14-19 a ga cewa Ɗan ne ke magana. Matiyu 3:16-17 na bayyana al’amarin bafismar Yesu. Ana gani anan Allah Ruhu Mai Tsarki na saukowa bisa Allah Ɗa yayin da Allah Uba na shelar jin daɗinsa cikin Ɗan. Matiyu 28:19 da 2Korantiyawa 13:14 sun zama misalai na mutum 3 dabam dabam cikin Triniti.

3) Membobi na Triniti an rarrabe su ɗaya daga wani cikin nassoshi iri iri. Cikin Tsohon Alƙawari “UBANGIJI” an rarrabe daga “Ubangiji” (Farawa 19:24; Yusha’u 1:4). “Ubangiji” na da “Ɗa” (Zabura 2:7,12; Misalai 30:2-4). An rarrabe Ruhu daga “UBANGIJI” (Littafin Lissafi 27:18) da kuma daga “Allah” (Zabura 51:10-12). An rarrabe Allah Ɗa da Allah Uba (Zabura 45:6-7; Ibraniyawa 1:8-9). Cikin Sabon Alƙawari, Yahaya 14:16-17 ita ce inda Yesu yayi magana ga Uba game da aikar da Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki. Wannan na nuna cewa Yesu bai ɗauki Kansa da zaman Uban ko kuma Ruhu Mai Tsarki ba. Ka lura kuma duk sauran lokatai cikin Linjila inda Yesu ke magana da Uba. Ko yana magana da kanSa ne? A’a. Yayi magana ga wani mutum cikin Triniti – Uban.

4) Kowanne memba na Triniti Allah ne: Uban Allah ne: Yahaya 6:27; Romawa 1:7; 1Bitrus 1:2. Ɗan Allah ne: Yahaya 1:2,14; Romawa 9;5; Kolosiyawa 2:9; Ibraniyawa 1:8; 1Yahaya 5:20. Ruhu Mai Tsarki Allah ne: Ayyukan Manzanni 5:3-4; 1Korantiyawa 3:16 (Shi wanda ke zama a ciki shine Ruhu Mai Tsarki Romawa 8;9; Yahaya 14:16-17; Ayyukan Manzanni 2:1-4).

5) Zama karkashi cikin Triniti: littafi ta nuna cewa Ruhu Mai Tsarki na karkashin Uba da Ɗa, kuma Ɗan na zama ƙarƙashin Uban. Wannan shine dangantakar ciki, kuma bata musuntar wa kowanne mutum da allahntakar Triniti ba. Wannan ita ce a sawwaƙe wurin wanda guntun tunanin mu zai iya ganewa da Allah marar iyaka. Game da Ɗan dubi: Luka 22:42; Yahaya 5:36; 20:21; 1Yahaya 4:14. Game da Ruhu Mai Tsarki dubi: Yahaya 14:16,26; 15:26; 16:7 kuma musamman Yahaya 16:13-14.

6) Ayyukan wani memba cikin Triniti: Uban shine tushe dukka ko sanadi na: 1) Sama da ƙasa (1Korintiyawa 8:6; Wahayin Yahaya 4:11); 2) Bayyanin Allah (Wahayin Yahaya 1:1); 3) Ceto (Yahaya 3:16-17); da kuma 4) ayyukan mutuntakar Yesu (Yahaya 5:17; 14:10). Uban ne ya yi sama duk da waɗannan abubuwa.

Ɗan shine wakili ta wanda Uban ke ayyuka na biye: 1) halitta da kiyaye duniya da sama (Farawa 1:2; Ayuba 26:13; Zabura 104:30); 2) bayyanin Allah (Yahaya 16:12-15; Afisawa 3:5; 2Bitrus 1:21); 3) Ceto (Yahaya 3:6; Titus 3:5; 1Bitrus 1:2); da kuma 4) ayyukan Yesu (Ishaya 61:1; Ayyukan Manzanni 10:38). Hakanan Uban ke yi duk waɗannan ta ikon Ruhu Mai Tsarki.

Babu wani sanannen misalai da suke da cikakken bayyani daidai na Triniti ba. Ƙwai (apple) ta kasa da nufin cewa ɓawon, fari, da kuma gwaiduwa sune sassan ƙwai, ba ƙwan ba ne cikin kansu. Uban, Ɗan da Ruhu Mai Tsarki ba sune sassan Allah ba, kowannensu Allah ne. Misalin ruwa na da ɗan kyau amma har yanzu ta kasa ta bayyana Triniti cikakke. Ruwa-ruwa,tururi, da kuma ƙanƙara sune siffofin ruwa. Uban, Ɗan, da kuma Ruhu Mai Tsarki ba sune siffofin Allah ba, kowannensu Allah ne. Hakanan, yayin da waɗannan misalai na yiwuwa su bamu hoton Triniti, hoton ba zama gaba ɗaya cikakke ba. Ba za a iya bayyana cikakke Allah marar iyaka ta misali mai iyaka ba. Maimakon a zura ido ga Triniti, a ƙoƙarta a zura ido kan batu na Girman Allah da halitta na rashin iyaka mafi tsawo da namu. “Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi! “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa wa ya taɓa bashi wata shawara?” (Romawa 11:33-34).

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke koyar game da Triniti?
© Copyright Got Questions Ministries