settings icon
share icon
Tambaya

Ko Yesu ne kaɗai hanya zuwa sama?

Amsa


”Bisa ga asali ni mutum nagari ne, don haka zan je sama.”“Shi ke nan, haka nan, ina waɗansu mugayen abubuwa, amma na fi yin abubuwan kirki, don haka zan je sama.”“Allah ba zai aikar dani zuwa jahannama don kawai ban yi rayuwa bisa ga Littafi Mai Tsarki ba. Zamanai sun sake!”“Sai mugayen mutane da gaske ne kaɗai kamar masu fitinad da yara da kuma masu kisan kai ne zasu je jahannama.”

Waɗannan duk sune tunanin gama-gari tsakanin yawancin mutane, amma gaskiyar ita ce, dukkansu ƙarairai ne. Shaiɗan, mai mulkin duniya, ya shuka waɗannan tunani a cikin kawunanmu. Shi, da kowane da ke bin hanyoyinsa, ya zama maƙiyi ga Allah (1 Bitrus 5:8). Shaiɗan kullum yana bad da kamansa kamar nagari (2 Korantiyawa 11:14), amma yana da iko bisa dukkan hankulan da basu zama na Allah ba.” Shaiɗan , allah na wannan mugun duniya, ya makantad da hankulan waɗancan da basu gaskata ba, da haka basu iya ganin mashahurin hasken Bishara wanda ke haskaka akansu. Basu fahimce sako game da ɗaukakar Kiristi, wanda yake ainihin kamanin Allah” (2 Korantiyawa 4:4).

Ya zama ƙarya ce a gaskata cewa Allah baya kulawa game da ƙananan zunubai, kuma cewa an keɓe jahannama don”mugayen mutane.” Duk zunubi yana raba mu daga Allah, har ma da”ƙaramin farar ƙarya.” Kowa yayi zunubi, kuma babu ko daya wanda yake nagari isasshe ya samu zuwa sama ta kansa (Romawa 3:23). Samun zuwa cikin sama bai dangana kan ko ayyukan kirki namu sun fi nauyin mugayen ba, mu duk zamu rasa idan al’amarin haka ne.”In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga aikin lada ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri bane kuma” (Romawa 11:6). Ba zamu iya yin kome nagari da zai bamu ladan aiki ga tafarki zuwa sama ba (Titus 3:5).

“Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa halaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa (Matiyu 7:13). Ko ma idan kowane yana rayuwar zunubi, amincewa da Allah ba zai zama abin farin jini ba, Allah ba zai gafarta da haka ba.” Waɗanda da kuke ciki, kuna biye wa al’amarin duniya nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskan nan da ke zuga zuciyar kangararru a yanzu” (Afisawa 2:2).

Sa’anda Allah ya halicce duniya, ta zama kammalalle. Kome yana da kyau. Sa’anan ya halicce Adamu da Hawa’u, ya basu tasu ƴancin son ransu, don su iya zaɓa ko zasu bi kuma da yi biyayya ga Allah ko babu. Amma Adamu da Hawa’u, ainihin farkon mutanen da Allah yayi, suka jarrabtu daga Shaiɗan da yi rashin biyayya ga Allah, kuma suka yi zunubi. Wannan ya raba su ( da kowanne da ya biyo bayansu, har da mu) daga iya samun wata dangataka mai kurkusa tare da Allah. Shi kamili ne, da tsarki, kuma dole ne ya shar’anta zunubi. A matsayin masu zunubi, ba zamu iya kaiwa can da kanmu ba. Don haka, Allah yayi hanyar da za’a haɗa mu da shi cikin sama.” Saboda ƙaunar da Allah yayi wa duniya har ya bada makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami” (Yahaya 3:16).”Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami cikin Alamsihu Yesu Ubangijinmu” (Romawa 6:23). An haifi Yesu don ya iya koya mana tafarkin kuma ya mutu don zunubanmu don kada mu yi mutuwar. Kwana uku bayan mutuwarsa, ya tashi daga kabari (Romawa 4:25), ya jarraba kansa mai nasara bisa mutuwa. Ya gina gada kan gurbi tsakanin Allah da mutum don mu iya samun dangataka na kai tsaye tare da shi idan da kaɗai zamu gaskata.

“Rai madawwami kuwa, shine su san ka, Allah makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko (Yahaya 17:3). Yawancin mutane sun gaskata da Allah, ko Shaiɗan ma yana yin haka. Amma a karɓi ceto, dole ne mu juyo ga Allah, a siffata dangataka na mutum da kansa, a juyo daga zunubanmu kuma a bi shi. Dole ne mu amince cikin Yesu da komene ne da muke da shi da kuma komene ne da muke yi.” Adalcin nan na Allah, wanda ke samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almsihu, na masu bada gaskiya ne dukka, ba kuwa bambanci” (Romawa 3:22). Littafi Mai Tsarki ta koyar cewa babu wata hanya ga ceto banda ta wurin Kiristi. Yesu na cewa cikin Yahaya 14:6”Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.”

Yesu ne kaɗai hanyar ceto domin shi ne kaɗai hanya ɗaya wanda zai iya biya mana hukuncin zunubanmu (Romawa 6:23). Babu wani addini mai koyar da zurfi ko tsananin zunubi da abubuwan da zai haifar. Babu wani addinin da yana miƙa biyarwar zunubi marar iyaka da Yesu Kiristi ne kaɗai ke iya tanadar. Babu wani”mai kafa addini” da yake Allah da ya zama mutum (Yahaya 1:1,14) - hanya kaɗai da za a biya bashi marar iyaka. Yesu sai da ya zama mutum don ya iya mutuwa. Ceto yana samuwa kaɗai ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi!” ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniya nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne zamu sami ceto” (Ayyukan Manzanni 4:12).

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Yesu ne kaɗai hanya zuwa sama?
© Copyright Got Questions Ministries