Tambaya
Mece ce Littafi Mai Tsarki ta faɗa game da da auren wata kablia?
Amsa
Dokar Tsohon Alƙawari ta umarci Isra’ilawa kar su shiga cikin auren wata kabila (Maimaitawar Shari’a 7:3-4). Dalilin wannan shine cewa Isra’ilawa za a ɓatar dasu daga Allah idan sun yi aure da masu bautar gumaka, matsafa, ko arna. An saka ƙa’ida iri ɗaya cikin Sabon Alƙawari, amma a wata mataki na dabam: “Kada kuyi cuɗanya marar dacewa da marasa bada gaskiya. To, me ya haɗa aikin adalci da na mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?” (2Korantiyawa 6:14). Daidai yadda Isra’ilawa (masu bada gaskiya ga Allah guda ɗaya) an umarce su kar su auri marasa bada gaskiya, haka ma Kiristoci ( masu bada gaskiya ga Allah guda ɗaya) ana umarta kar su auri marasa bada gaskiya. Da a amsa wannan tambaya takamaimai, a’a, Littafi Mai Tsarki bata faɗi cewa auren wata kabila laifi ne ba.
A shari’anta mutum ta halin sa/ta, ba ta launin fata ba. Dukkanmu kamata yayi muyi hattara kar mu nuna fin so ga wasu, ko nuna son wane ko kabila ga wasu (Yakubu 2:1-10), dubi musamman ayoyi 1 da 9). Ma’aunin Kirista namiji ko mace don zaɓen abokin zama ya zama kullum a gano idan wanda suke da sha’awa shi Kirista ne (2Korantiyawa 6:14), wani ne wanda an sake haifuwa ta bangaskiya cikin Yesu Kiristi (Yahaya 3:3-5). Bangaskiya cikin Kiristi, ba launin fata ba, ita ce ma’aunin Littafi Mai Tsarki don zaɓen abokin aure. Auren wata kabila ba aba ce na daidai da rashin daidai ba, amma na hikima ne, basira, da kuma addu’a.
Dalili kaɗai da za a lura da auren wata kabila da kyau shine domin matsalolin ma’aurata haɗa- kabila mai yiwuwa su samu saboda waɗansu zasu ji nauyin karɓarsu. Yawancin ma’auratar waɗansu kabila kan sami nuna tara da ba’a., sau tari har daga iyalai na kansu. Waɗansu ma’auratan wasu kabila kan sami matsaloli yayin da ƴaƴan su suna da launin fata dabam da ta iyayen da/ko kuma dangogin. Ma’auratan wasu kabila suna bukata su lura da waɗannan abubuwa da kuma a shirya dominsu, muddin sun yanke shawara suyi aure. Kuma, ko da yake, taƙurawa kaɗai da Littafi Mai Tsarki ta sa kan wanda yake Kirista a sha’anin aure shine ko wancan mutum ya zama memba na jikin Kiristi.
English
Mece ce Littafi Mai Tsarki ta faɗa game da da auren wata kablia?