settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da caca? Ko caca zunubi ne?

Amsa


Za a iya bada ma’anar caca kamar “kasadar da kuɗi cikin ƙoƙarin a riɓanya kuɗin kan wani abin da ke da rashin yiwuwa.” Littafi Mai Tsarki takamaiamai bata hukunta caca ba, yi fare, ko dai tambola. Littafi Mai Tsarki tana mana gargaɗi,amma dai, mu tsaya nesa can daga ƙaunar kuɗi (1Timoti 6:10; Ibraniyawa 13:5). Littafi kuma tana gargaɗe mu da mu tsaya nesa daga ƙoƙarin “yin arziki da sauri” (Misalai 13:11; 23:5; Mai Hadishi 5:10). Caca tabbatacce ta zura ido ne kan ƙaunar kuɗi kuma babu shakka na jarabar mutane da alƙawarin sauri da arzikin sauƙi.

Mene ne ba daidai ba da yin caca? Caca batu ne mai wuya don idan anyi ta cikin matsakaici kuma a wata sa’i, ya zama ɓad da kuɗi, amma bata zama lalle “sharri” ba. Mutane na ɓad da kuɗi kan ayyuka iri iri. Caca bata zama da fiye da ƙanƙanta na kashe kuɗi da ƙallon fim (cikin yawancin halaye), cin abinci mai tsada wanda ba na lalle ba, ko dai a sayi wani abin banza. A lokaci guda, batun cewa an ɓad da kuɗi kan wasu abubuwa bai baratad da caca ba. Bai kamata ɓad da kuɗi ba. Ya kamata a adana kuɗi mafi kima don amfanin gaba ko a bayar ga aikin Ubangiji- banda yin caca dasu.

Caca cikin Littfi Mai Tsarki: Yayin da Littfi Mai Tsarki a fili bata amfani da caca ba, ya amshi wasannin “sa’a” ko “ƙaddara.” Alal misali, anyi amfani da jefa ƙuri’a cikin Littafin Lissafi don a zaɓi tsakanin bunsurun hadaya da da wanda za a kora zuwa jeji da rai. Joshua ya jefa kuri’a don tabbatar rabe-raben kasa tsakanin ga kabilu dabam dabam. Nehemiya ya jefa ƙuri’a tabbatar da wanda zai yi zama cikin ganuwar Urushalima da wanda ba zai yi ba. Manzanni sun jefa ƙuri’a don tabbatar da mai ɗaukar matsayin Yahuda. Misalai 16:33 tana cewa, “mutane sukan jefa ƙuri’a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake bada amsa.” Babu inda cikin Littafi Mai Tsarki da caca ko “ƙaddara” anyi amfani da su don nishaɗi ko an nuna kamar abin yi karɓaɓɓe don mabiyan Allah.

Gidan wasannin caca da tambola: Gidan wasannin caca na amfani da kowaɗanne irin dabarun kasuwanci ta jan hankalin masu caca su kasadar da kuɗi masu yawa in ya yiwu. Kullum suna bada barasa da tsada ko na kyauta, wadda kan ƙarfafa buguwa, kuma sa’anan ya rage masu ƙarfin yanke shawarwari na hikima. Ana cikakken maguɗin kome a gidan wasannin caca don a kwashi masu yawa da bayar da ribar ba kome, banda cincirindo da nisaɗi ta wofi. Tambololi na ƙoƙarta nuna kansu kamar wata hanyar tallafin kuɗin ilimi da/ko shirye-shiryen jama’a. Amma dai, nazarce-nazarce sun nuna cewa masu yin tambola kullum mutane ne waɗanda aƙalla sukan iya sayi don kashe kudi kan tikitin tambola. Kwaɗayin “yin arziki da sauri” ya zama jaraba mafi girma da ba za a ƙi ba ga waɗanda sun ƙosa. Daman samun nasara suna nan ɗan kaɗan ne, wanda yana sakamakon rayukan mutane da dama kan rusa

Abin da yasa kuɗin tambola bata gamshi Allah ba: Mutane da dama na da’awa suna wasan tambola ko caca don cewa zasu iya bada kuɗin ga ikilisiya, ko kuma ga waɗansu sanadai masu kyau. Yayin da wannan mai yiwuwa ya zama wata dalili mai kyau, gaskiyar shine cewa ƴan ƙalila ne ke morar nasarorin caca don manuofin ibada. Nazarce-nazarce sun nuna cewa da yawan masu nasarar caca suna ma cikin matsalar kuɗi mafi muni shekaru kaɗan bayan samun ci mai tsoka fiye da yadda suke a dă can.

Kaɗan ne, in akwai ma, da gaske ke bada kuɗin ga wata sanadi mai kyau. Gaba kuma, Allah baya bukatar kuɗin mu don tallafar aikinsa cikin duniya ba. Misalai 13:11 tana cewa, “Dukiya da ka same ta a sawwaƙe, zaka rasa ta da sauri, amma wanda ya same ta da wahala, zata yi ta karuwa.” Allah mamallaki ne kuma zaya tanadar da bukatu na ikilisiya ta hanyoyin gaskiya. Za a ɗaukaka Allah ta karɓan taimakon kuɗin kwaya, ko kuɗin sata da aka ƙwace daga banki? Ko ma Allah ya bukaci ko ya so kuɗin da an “sato” daga matalauci ta jaraba don arziki.

1Timoti 6;10 tana gaya mana, “Ai, son kuɗi shine tushn kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, su jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukan rai.” Ibraniyawa 13:5 tana furtawa, “ Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke dashi, gama Allah kansa ya ce ‘Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” Matiyu 6:24 tana sanar, “ Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kua ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne Littafi Mai Tsarki ke faɗi game da caca? Ko caca zunubi ne?
© Copyright Got Questions Ministries