Tambaya
Waɗanne ne halayen Allah? Mene ne kamannin Allah?
Amsa
Albishir, kamar yadda muke ƙoƙarta mu amsa wannan tambaya, ya zamana akwai da yawa da za’a iya gano game da Allah! Waɗannan waɗanda suna jaraba wannan mai yiwuwa ne da farko su same shi da taimako a karanta har ƙarshe duka; sa’annan a koma baya kuma a dubi zaɓaɓɓun nassoshin Littafi Mai Tsarki don ƙarin bayyani kuma. Nassoshin Littafi Mai Tsarki gaba ɗayan su suna da muhimmanci, gama in ban da ikon Littafi Mai Tsarki ba, karo- karon waɗannan kalmomi ba zasu fi ra’ayin mutum ba; wanda a kanta sau da yawa baya daidai cikin ganewar Allah ( Ayuba 42:7). Da a faɗi cewa yana da muhimmanci gare mu mu gwada gane da abin da yake Kaman Allah ya zama kamar ƙaton bayani marar isa! Rashin yin haka nan zai zama mai yiwuwa ne sanadin kafuwa, bi baya, da kuma sujada ga allolin ƙarya saɓani da nufin Sa (Fitowa 20:3-5).
Sai kawai abin da Allah ya zaɓar don kan Sa a bayyana za’a iya sani. Ɗaya daga cikin halayen Allah ko ƙwarinsa shine “Haske” ma’ana cewa shine mai bayyana kan sa cikin labari na kan sa (Ishaya 60:19; Yakubu 1:17). Bias gaskiya da cewa Allah ya bayyana sanin Sa bai kyautu a ƙyalle ba, kada wani namu ya kasa shiga hutun sa (Ibraniyawa 4:1). Halitta, Littafi Mai Tsarki, kuma Kalmar ta zama tsoka (Yesu Kiristi) zasu taimake mu mu san abin da kamar Allah yake.
Bar mu fara da fahinta cewa Allah ne Mahaliccin mu kuma cewa mun zama bangare na halittarsa (Farawa 1:1; Zabura 24:1). Allah ya faɗi cewa an halicci mutum cikin kamannin sa. Mutum yana bisan sauran halitta kuma an bashi mulki akan ta (Farawa 1:26-28). Halitta ta ɓaci ta wurin “faɗuwa” amma har yau tana nuna tsinkayo na ayyukan sa (Farawa 3:17; Romawa 1: 19-20). Da yin lura da ƙatuwar halitta, wuya, da kyau, da kuma tsari zamu iya samun tunani na al’ajabin Allah.
Karatun waɗansu sunaye na Allah zai iya taimaka cikin nemar mu na abin da kaman Allah yake. Suna nan kamar haka:
Elohim – Mai Ƙarfi, na Allah ( Farawa 1:1)
Adonai¬¬ - Ubangiji, mai isharar dangantakar maigida ga bawa (Fitowa 4:10,13)
El Elyon - Mafi ƙasaitacce, mai ƙarfi dukka (Farawa 14:20)
El Roi - Ƙaƙƙarfa wanda yake gani (Farawa 14:20)
El Shaddai - Allah maɗaukaki (Farwa 17:1)
El Olam – Allah madawwami (Ishaya 40:28)
Yahweh – UBANGIJI “NI NE” ma’ana Allah mai kasancewa da kansa har abadan Fitowa 3:13,14).
Yanzu zamu ci gaba da dudduba ƙarin halayen Allah; Allah madawwami ne, ma’ana bashi da farko kuma da cewa kasancewar sa ba zai taba ƙarewa ba. Shi marar mutuwa ne, marar iyaka (Maimaitawar Shari’a 33:27; Zabura 90:2; 1Timoti 1:17). Allah marar sakewa ne, ma’ana Shi baya canzawa; wannan na nufin cewa gaba ɗaya matabbaci ne da amintacce ( Malakai 3:6; Littafin Lissafi 23:19; Zabura 102:26,27). Allah baya kwantantuwa, ma’ana babu wani kamarsa cikin ayyuka da kasancewa; baya da madaidaici kuma cikakke ne (2 Samuila 7:22; Zabura 86:8; Ishaya 40:25; Matiyu 5:48). Allah baya bincikuwa, ma’ana Shi baya fahintuwa, biɗuwa, ya wuce gaban samuwa gaba ɗaya cikin ganewa da shi (Ishaya 40:28; Zabura 145:3; Romawa 11:33,34).
Allah mai adalci ne, ma’ana shi baya nuna tara ga mutane da azanci na nunan gatanci (Maimaitawar Shari’a 32:4; Zabura 18:30). Allah mai iko dukka ne, ma’ana shine mafi iko dukka; zai yi kome da ya gamshe shi, amma ayyukansa suna kullum da sauran halayen sa (Wahayin Yahaya 19:6; Irmiya 32:17,27). Allah yana koina, ma’ana yana nan ko da yaushe, koina; wannan bai nuna cewa Allah ya zama kome da kome ba (Zabura 139:7-13; Irmiya 23:23). Allah masanin dukka ne, ma’ana ya san da, yanzu, da gaba, har ma da abin da muke tunani a kowace lokaci; tun da yake ya san kome, kullum zai gudanar da shari’arsa da adalci (Zabura 139:1-5; Misalai 5:21).
Allah ɗaya ne, ma’ana ba wai kawai cewa babu wani dabam, amma kuma cewa shine kaɗai ke iya biyan bukatu mafi zurfi da kewar zukatanmu, kuma shi kaɗai ne ya cancanci sujadarmu da addu’armu (Maimaitawar Shari’a 6:4). Allah mai adalci ne, ma’ana cewa Allah ba zai iya kuma ba zai shige kan saɓo ba; ya zama domin adalcinsa da gaskiyarsa ne cewa zunubanmu sun sami gafartawa, da Yesu ya ji da hukuncin Allah sa’anda aka ɗora masa zunubanmu (Fitowa 9:27; Matiyu 27:45-46; Romawa 3:21-26).
Allah ne kan kome da kowa, ma’ana shine maɗaukaki; dukkan halittarsa ga baki ɗaya, ko cikin sani ko da rashin sani, ba zata iya tauye manufofin sa ba ( Zabura 93:1; 95;3; Irmiya 23:20). Allah ruhu ne, ma’ana shi baya ganuwa (Yahaya 1:18; 4:24). Allah Triniti ne, ma’ana shi uku ne cikin ɗaya, ɗaya ne cikin ainihinsa, tsara ne cikin iko da ɗaukaka. A lura cewa a cikin farkon nassin Littafi Mai Tsarki da aka ja cewa ‘suna’ ɗaya ce ko da yake ta nuna mutum uku dabam dabam ne- “Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki” (Matiyu 28:19-21; Markus 1:9-11). Allah gaskiya ne, ma’ana cewa ya yarda da dukkan abin da shi yake, zai tabbata marar ruɓewa kuma ba zai iya yin ƙarya ba (Zabura 117:2; 1Samuila 15:29).
Allah mai tsarki ne, ma’ana cewa yana a raɓe daga dukkan ƙazantar halin kirki kuma yana abokin gaba zuwa gare ta. Allah yana ganin dukkan mugunta kuma tana fusatar da shi; kullum ana ambaton wuta cikin Littafi Mai Tsarki tare da tsarki. Ana nuna Allah da kamar wuta mai cinyewa (Ishaya 6:3; Habakuk 1:13; Fitowa 3:2,4,5; Ibraniyawa 12:29). Allah mai alheri ne- wannan ya ƙunsa nagarta, kirki, rahama, da ƙauna- waɗanda su kalmomi ne masu launin ma’anoni ga nagartarsa. In ba don alherin Allah ba da ya zamanto sauran halayen sa zasu ware mu daga wurin sa. Abin godiya wannan ba shine al’amarin ba, gama yana sha’awar ya san kowannenmu da kansa (Fitowa 34:6; Zabura 31:19; 1Bitrus 1:3; Yahaya 3:16; Yahaya 17:3).
Wannan ita ce kaɗai gwaji mai dama-dama da za a amsa tambaya mai girma irin ta Allah. Don haka ka ƙarfafa kwarai ka ci gaba da biɗarsa (Irmiya 29:13).
English
Waɗanne ne halayen Allah? Mene ne kamannin Allah?