Tambaya
Mece ce Littafi Mai Tsarki ta ce game da luwaɗi?
Amsa
Littafi Mai Tsarki akai akai tana gaya mana cewa aikata luwaɗi zunubi ne (Farawa 19:1-13; Littafin Firistoci 18:22; Romawa 1:26-27; 1Korantiyawa 6:9). Romawa 1:26-27 tana koya kai tsaye cewa luwaɗi ya zama sakamakon musunta da yin rashin biyayya ga Allah. Sa’anda mutum ya ci gaba cikin zunubi da rashin ibada, Littafi Mai Tsarki tana faɗi mana cewa Allah “ ya sallama su ga rashin tsarkaka” ga ma ƙarin mugunta da zunubi ɗungum garin a nuna masu rashin fa’ida da rashin bege na rayuwa ba tare da Allah ba. 1Korantiyawa 6:9 tana furtawa cewa “maƙetata” ƴan luwaɗi ba zasu sami gado a mulkin Allah ba.
Allah bai halicci mutum da sha’awar luwaɗi ba. Littafi Mai Tsarki na faɗi mana cewa mutum yakan zama dan luwaɗi don zunubi (Romawa 1:24-27), kuma a ƙarshe domin zabi na kansu. Mai yiwuwa a haifi mutum da laulayi mafi na luwaɗanci, daidai yadda ana haifar mutane da halin gwada fin ƙarfi da waɗansu zunubai. Wannan ba hujja ba ce ga wanda ya zaɓi yin zunubi ta sallamar wa cikin sha’awoyin zunubansu. Idan an haifi mutum da laulayi mafi ga fushi/ fusata, wannan ya mai da ita daidai ne su tsinduma cikin waɗannan muradai? Ko kadan babu! Gaskiyar daya ce ga luwaɗanci.
Duk da haka, Littafi Mai Tsarki bata gwada luwaɗanci kamar zunubi “mafi” akan waɗansu ba. Dukkan zunubi laifi ne ga Allah. Luwaɗanci ɗaya ne kawai daga jerin masu yawa cikin 1Korantiyawa 6:9-10 cewa zasu iya raba mutum daga mulkin Allah. Bisa ga Littafi Mai Tsarki, gafarar Allah tana daidai a yalwace ga ɗan luwaɗi yadda take ga mazinaci, mai bautar gumaka, mai kisan kai, barawo, da dai sauransu. Allah kuma yayi alƙawarin ƙarfi don nasara bisa zunubi, haɗe da luwaɗanci, ga duk waɗancan waɗanda zasu gaskata cikin Yesu Kiristi don ceton su (1Korantiyawa 6:11; 2Korantiyawa 5:17).
English
Mece ce Littafi Mai Tsarki ta ce game da luwaɗi?