settings icon
share icon
Tambaya

Wace ce matar Kayinu? Ko matar Kayinu ƴar’uwarsa ce?

Amsa


Littafi Mai Tsarki ba ta faɗa takamaimai wace ce ta zama matar Kayinu ba. Amsa kaɗai mai yiwuwa ita ce kila matar Kayinu ƴar’uwarsa ce, ko ƴar kanwa ko ƴar ƴar ƙanwa, da dai sauransu. Littafi Mai Tsarki bata faɗi ko shekarun Kayinu nawa ne sa’anda ya kashe Habila (Farawa 4:8).

Tun da yake dukkansu manoma ne, mai yiwuwa dukkansu manya mutane ne, kila da iyalai na kansu. Adamu da Hawwa’u bisa gaskiya suna da ƙarin yara banda kawai Kayinu da Habila a lokacin da an kashe Habila – farilla suna da ƙarin yara masu yawa daga baya (Farawa 5:4). Gaskiya shine cewa Kayinu yana tsoron ran sa bayan ya kashe Habila (Farawa 4:14) ta nuna cewa mai yiwuwa akwai da yawa waɗansu yara kuma watakila har da jikokki ko tattaɓa -kunne na Adamu da Hawwa’u a lokaci nan. Matar Kayinu (Farawa 4:17) ta zama ɗiya ce ko jikanyar Adamu da Hawwa’u ne.

Tun da yake Adamu da Hawwa’u suna na farko (kuma kaɗai ) na bani adam, ƴaƴansu bisa da wata zaɓi sai dai su auri junansu. Allah bai haramta auratayya cikin iyali ba sai daga baya can sa’anda akwai isassun mutanen da aure cikin iyali bai zama lalle ba (Littafi Firistoci 18:6-18). Dalilin da yasa auren haram kullum na kawo cututtukan jini cikin yara shine cewa sa’anda mutane biyu masu ƙwayoyin jini iri ɗaya (wato ɗan’uwa da ƴar’uwa ) suna da yara –cututtukan jini suna mai yiwuwa su auku sosai don duk iyayen suna da cututtukan kan su. Sa’anda mutane sun fito daga iyalai dabam dabam suna da yara – yana zama da rashin yiwuwa sosai cewa duk iyayen zasu zama da da cutar ƙwayar jini iri ɗaya. Tsarin ƙwayar jinin mutum tana ƙara “ƙazanta” a ƙarnin baya baya nan yayin da cutar ƙwayoyin jini suna yaɗuwa, ƙarfafawa, da kuma isarwa daga tsara zuwa tsara. Adamu da Hawwa’u basu da wata cutar ƙwayoyin jini ba, haka nan, wannan ya taimaka masu da kuma ƴan farkon tsararraki na zuriyarsu da samun nau’i mafi na kiwon lafiya fiye da namu yanzu. Ƴaƴan Adamu da Hawwa’u suna da kadan, in da akwai, cutar ƙwayoyin jini. A sakamakon haka, ya zama da rashin haɗari su auri junansu.. takan yiwu ta zama baƙuwar abu ko ma da ƙyama ayi tunanin matar Kayinu da zama ƴar’uwarsa. A cikin farko, tun da Allah ya fara da mutum guda da mace guda, tsara na biyu ba zasu zama da zaɓi ba amma dai suyi auratayya a tsakankanin junansu.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Wace ce matar Kayinu? Ko matar Kayinu ƴar’uwarsa ce?
© Copyright Got Questions Ministries