settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne ke faruwa bayan mutuwa?

Amsa


Tambaya mene ne ke faruwa bayan mutuwa takan iya zama da rikitarwa. Littafi Mai Tsarki bata bayyana a fili kan lokacin da mutum zai kai ƙarshen ƙaddararsu ta har abada ba. Littafi Mai Tsarki ta faɗa mana cewa bayan loton mutuwa, a kan ɗauki mutum zuwa sama ko jahannama bisa ko shi ko ita da ma ya karɓi Kiristi a matsayin mai ceton sa/ta. Ga masu bangaskiya, bayan mutuwa shine rabuwa daga jiki da kasancewa tare da Ubangiji (2 Korantiyawa 5:6-8; Filibiyawa 1:23). Ga marasa bangaskiya, bayan mutuwa na nufin hukuncin har abada cikin Jahannama (Luka 16:22-23).

Nan ne ya kan iya zama da rikitarwa akan mene ne ke faruwa bayan mutuwa. Wahayin Yahaya 20:11-15 ta kwatanta duk wadannan da ke Jahannama da aka jefar cikin tafkin wuta. Wahayin Yahaya 21-22 ta kwatanta Sabuwar Sama da Sabuwar Duniya. Don haka, da alama cewa har sai ga tashin matattu na ƙarshe, bayan mutuwa mutum yana zama ne cikin Sama da Jahannama na “wucin gadi.” Ƙaddarar har abada mutumin ba zai sake ba, amma ainihi “wurin zama” na ƙaddarar har abada na mutumin zai sake. A wani sa’i bayan mutuwa, marasa bada gaskiya za a jefar da su cikin tafkin wuta (Wahayin Yahaya 20:11-15). Waɗannan sune ƙaddarar ƙarshe na har abada na dukkan mutane –dangane gaba ɗaya ko mutum ya amince da Yesu Kiristi kaɗai don ceto na zunubansu.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne ke faruwa bayan mutuwa?
© Copyright Got Questions Ministries