settings icon
share icon
Tambaya

Ko Littafi Mai Tsarki ta koyar da tsarewa ta har abada?

Amsa


Sa’anda mutane sun san Kiristi a matsayin mai ceton su, sun shigo ne cikin dangantaka tare da Allah da ya basu tabbacin rai madawwami. Yahuza 24 tayi shela, “Ga wanda ke da iko ya tsare ku daga faɗuwa, ya kuma miƙa marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙa da farin ciki.” Ikon Allah tana iya ta riƙe mai bada gaskiya daga faɗuwa. Ya saura gare shi, ba gare mu ba, ya miƙa mu a gaban ɗaukakarsa mai daraja. Tsarewarmu ta har abada ta zama sakamakon Allah ne mai riƙonmu, ba mu bane masu kulawa da cetonmu ba.

Ubangiji Yesu Kiristi yayi shela, “ ina basu rai madawwami, ba kuwa zasu halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. Ubana, wanda ya bani su, yafi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban” (Yahaya 10;28-29b). Duk da Yesu da Uban sun riƙe mu kankan cikin hanun su.Wanene ya yiwu ya iya raba riƙewar duk Uban da Ɗan? Afisawa 4:30 tana gaya mana cewa masu bada gaskiya an “hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa.” Idan masu bada gaskiya basu da tsarewar har abada ba, hatimcewa bata iya yiwuwa na gaske a ranar fansa ba, amma kaɗai ga ranar zunubi, fanɗarewa, ko rashin ibada. Yahaya 3:15-16 na faɗi cewa duk wanda ke bada gaskiya cikin Yesu Kiristi zai “sami rai madawwami.” Idan da za a yi wa mutum alƙawarin rai madawwami, amma kuma a ɗauke ta, bata zama “madawwami” ba ce tun farko ma. Idan tsarewa ta har abada ba gaskiya ba ce, alƙawaran rai madawwami cikin Littafi Mai Tsarki zasu zama cikin kuskure.

Gardama mafi ƙarfi don tsarewa ta har abada shine Romawa 8:38-39, “Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, ko tsawo, ko zurfi, kai ko kowace irin halitta ma, ba zasu iya raba mu da ƙaunar da Allah ke yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.” Tsarewarmu ta har abada ta zauna ne kan ƙaunar Allah ga waɗanda Shi ya fanshe su. Tsarewarmu ta har abada Kiristi ne ya saye ta, alƙawarin Uba, da hatimcewar Ruhu Mai Tsarki.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Ko Littafi Mai Tsarki ta koyar da tsarewa ta har abada?
© Copyright Got Questions Ministries