settings icon
share icon
Tambaya

Mece ce ra’ayin kirista na mutum ya kashe kansa? Mene ne Littafi Mai Tsarki ke fadi game da mutum ya kashe kansa?

Amsa


Bisa ga Littafi Mai Tsarki, ko da mutum ya kashe kansa ba shine abin da zai ƙudurta ko shi ko ita zai sami shiga cikin sama ba. Idan mara bada gaskiya ya kashe kansa, shi ko ita bai yi kome ba amma “‘ƙarin saurin” tafiyar su ne zuwa tafkin wuta. Duk da haka, mutumin da ya kashe kansa a ƙarshe zai yi zama a cikin Jahannama don ƙin ceto ta wurin Kiristi, ba don sun kashe kansu ba ne. Littafi Mai Tsarki ta ambaci mutum biyar kai tsaye waɗanda sun kashe kansu: Abimelek (Littafin Mahukunta 9:54), Saul (1Samuila 31:4), mai ɗaukar wa Saul makamai (1Samuila 31:4-6), Ahitofel (2Samuila 17:23), Zimri (1Sarakuna 16:18) da kuma Yahuda (Matiyu 27:5). Kowannensu da ma mugu ne, mutane masu zunubi (babu isasshen abin da aka faɗa game da mai riƙe wa Saul makamai da zamu shari’anta halinsa). Wasu suna duban Samson wanda ya kashe kansa (Littafin Mahukunta 16:26-31), amma maƙasudin Samson shine ya kashe Filistiyawa, ba kansa ba ne. Littafi Mai Tsarki na kallon mutum ya kashe kansa daidai ne da kisan kai - shine abin da ya zama – kashe kanka. Allah shine wanda zai yanke shawara lokacin da kuma yaya ne mutum zai mutu. Ka ɗauki ikon nan cikin hannayenka , bisa ga Littafi Mai Tsarki, ya zama saɓo ne ga Allah.

Mece ce Littafi Mai Tsarki tan faɗi game da Kirista wanda ya kashe kansa? Ban gaskata cewa mai bada gaskiya da ya kashe kansa zai rasa ceton kuma ya tafi jahannama ba. Littafi Mai Tsarki tana koyar cewa daga loton da mutum ya gaskata da gaske cikin Kiristi, shi ko ita an tsare shi har abada (Yahaya 3:16). Bisa ga Littafi Mai Tsarki, Kiristoci zasu iya sani banda shakka cewa sun mallaki rai madawwami komene ne ya faru. “Na rubuto muku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Dan Allah, domin ku tabbata kuna da rai mdawwami” (1Yahaya 5:13). Babu abin da zai raba Kirista daga ƙaunar Allah! “Domin na tabbata, ko mutuwa ce, ko rai, ko mala’iku, ko manyan mala’iku, ko al’amuran yanzu, ko al’amura masu zuwa, ko masu iko, ko tsawo, ko zurfi, kai ko kowace irin halitta ma, ba zasu iya raba mu da ƙaunar da Allah ke yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba” (Romawa 8:38-39). Idan ba wani “halittaccen abu” da zai iya raba Kiristoci da ƙaunar da Allah, kuma har ma da Kirista wanda ya kashe kansa ya zama ‘halittaccen abu” sa’anan ba ma mutum ya kashe kansa zai iya raba shi daga ƙaunar Allah ba. Yesu, ya mutu don dukkan zunuban mu... kuma idan Kirista na gaske zai, a lokacin faɗawa da raunin ruhu, kashe kansa – wannan zai zama zunubi ne wanda Yesu ya mutu domin ta.

Wannan ba wai a ce mutum ya kashe kansa ba zunubi ne mai tsanani a gaban Allah ba. Bisa ga Littafi mai Tsarki, mutum ya kashe kansa kisan kai ne, laifi ne koyaushe. Zan zama da tsananin shakku game da ingancin bangaskiyar kowanne wanda na da’awar zama Kirista duk da haka ya kashe kansa. Babu wata halin da kake ciki da zai kuɓutar da wani wanda musamman Kirista, ya ɗauki ransa ko ranta. An kira Kirista suyi rayuwansu ga Allah- yanke shawara kan loton mutuwa na Allah ne kuma nasa kaɗai. Watakila hanya mai kyau na kwatanta mutum ya kashe kansa wa Kirista zai zama daga Littafin Esta. A cikin Farisa, suna da wata dokar da kowane wanda ya zo gaban Sarki ba tare da gayyata ba, za a iya kashewa sai dai Sarki ya miƙa sandansa wajen mutumin- alamar jinƙai. Mutum ya kashe kansa ga Kirista zai zama ka kutsa kanka ga Sarki maimakon a jira gareshi ya kirawo ka. Zai miƙo sandansa gareka, ya tsirad da rai madawwami naka, amma wannan bai nuna yana murna da kai ba. Ko da yake bai kamata mutum ya kashe kansa ba, ayar Littafi Mai Tsarki 1Korantiyawa 3:15 yana yiwuwa bayyani mai kyau ne ga abin da yakan faru da Kirista da ya kashe kansa:” Ko da yake shi kansa zai cetu, amma kamar ya bi ta wuta ne.”

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mece ce ra’ayin kirista na mutum ya kashe kansa? Mene ne Littafi Mai Tsarki ke fadi game da mutum ya kashe kansa?
© Copyright Got Questions Ministries