Tambaya
Wane ne Yesu Kiristi?
Amsa
Wanen ne Yesu Kiristi? Ba kamar tambayar, “ Ko akwai Allah?” Mutane ƙalila ainun suna tambaya ko Yesu Kiristi yana nan. Gaba ɗaya an yarda cewa Yesu ya zama mutum da gaske wanda yayi tafiya a bisa duniya a cikin Isra’ila kusan shekaru 2000 da suka wuce. Gardama takan fara ne sa’anda ana zancen fanni na cikakken shaidar Yesu. Kusan kowace babbar addini tana koyar cewa Yesu annabi ne, ko malamin kirki, ko dai mutum mai imani. Damuwar ita ce, Littafi Mai Tsarki tana gaya mana cewa Yesu bila haddin yafi wani annabi, malamin kirki, ko mutum mai imani.
C.S. Lewis a cikin littafin sa ya rubuta waɗannan: “Ina ƙoƙari anan in hana kowane daga faɗin anihin wautar abu da mutune safai kan ce game da Shi (Yesu Kiristi): “Ina a shirye in yarda Yesu a matsayin babban malamin halin kirki, amma ban yarda da da’awar sa na zaman Allah ba.” Wannan ita ce abu ɗaya da bai kamata mu faɗi ba. Mutumin da yake mutum ne kawai, kuma ya faɗin irin abubuwan da Yesu ya faɗe su da bai zama babban malami halin kirki ba. Da ya zama ko a ce mahaukaci--- a kan matakai da mutum wanda yana cewa Shine dafaffen ƙwai ---ko dai shi ya zama Shaiɗan na Jahannama. Dole kayi zaɓin ka. Ko wannan mutum ya zamo, kuma ya zama, Ɗan Allah, ko dai mahaukaci ko wani abu mai muni --- Zaka iya rufe shi kan wawa ne, zaka iya tofa masa yau kuma ka kashe shi kamar aljanni; ko kuma ka faɗi a kafafuwar sa kuma ka kira Ubangiji da kuma Allah. Amma kar mu taho da wata gaggarumar rashin hankali game da zaman sa mutum babban malami. Bai bar wannan zaɓi gare mu ba. Bai nufa da haka ba.”
Haka, wane ne Yesu yake da’awa ya zama? Wane ne Littafi Mai Tsarki ta ce Shi ya zama? Da farko, bar mu dubi kalmomin Yesu cikin Yahaya 10:30, “ Ni da Uba daya muke.” A tsinkayon farko, wannan ba mai yiwuwa ne ya zama da’awa na zaman Allah ba. Duk da haka, dubi yanda Yahudawa suka amsa da furcin sa, “ Ba don wani aikin nagari zamu jajjefe ka ba, sai dai don sabo, don kai, ga kamutum, amma kana mai da kanka Allah” (Yahaya 10:33). Yahudawa sun gane da furcin Yesu da zama da’awa shi Allah ne. A cikin ayoyi na biye, Yesu bai taɓa gyarta wa Yahudawa ta cewa, “ Ban yi da’awa na zaman Allah ba.” Wannan na nufin Yesu da gaske na cewa Shi Allah ne ta furtawa, “Ni da Uba daya muke” (Yahaya 10:30). Yahaya 8:58 ta zama wata misali kuma. Yesu yayi shela, “ Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.” Har ila dai, cikin amsawa, Yahudawa sun kwashi duwatsu da ƙoƙarin a jajjefi Yesu, (Yahaya 8:58). Yesu ya sanar da shaidar sa a matsayin “Ni ne” ya zama shafa kai tsaye ne na sunan Allah cikin Tsohon Alkawari (Fitowa 3:14). Me yasa Yahudawa kuma zasu so su jajjefe Yesu idan da bai fai wani abin da sun gaskata da zaman sabo, wato, da’awar zaman Allah?
Yahaya 1:1 tana cewa, “Kalma nan kuwa Allah ne.” Yahaya 1:14 tana cewa “Kalman nana kuwa ya zama mutum.” Wannan a fili na nufin cewa Yesu Shine Allah cikin tsoka. Toma almajiri ya furta ga Yesu, “Ya Ubangijina, Allah na kuma!” (Yahaya 20:28). Yesu bai yi masa gyara ba. Manzo Bulus ya kamanta Shi da kamar “---Allahnmu Mai Girma, Mai Ceto Yesu Almasihu” (Titus 2:13). Manzo Bitrus yayi faɗi kan abu ɗaya, “--- Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi” (2 Bitrus 1:1). Allah Uba ya zama mashaidi na cikakken shaidar Yesu ma, “Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne, Sandan sarautarka sanda ne na tsantsar gaskiya.” Annabtan Tsohon Alkawari game da Kiristi na sanar da Allahntakarsa, “Gashi, an haifa mana ɗa! Mun sami Yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci, Mai Al’ajabi,” “Allah Maɗaukaki.” “Uba Madawwami.” “Sarkin Salama.”
Haka, kamar yadda C.S. Lewis yayi gardama, gaskatawa ga Yesu da zaman malamin kirki ba zaɓi ba ne. Yesu a fili kuma da rashin shakka yayi da’awar zaman Allah. Idan shi ba Allah ba, sa’anan Shi maƙaryaci ne, kuma saboda haka ba annabi ba ne, ba malamin kirki ba ne, ko dai ba mai imani ba ne. A ƙoƙarin yin musun kalmomin Yesu, “masanan” zamani ta yau sun ɗauki “Yesu na gaskiya cikin tarihi” bai faɗe yawancin abubuwan da Littafi Mai Tsarki ta shafa masa ba. Wane mu muyi gardama da maganar Allah game da abin da Yesu yayi ko bai ce ba? Yaya “masani” zai iya cire bayan shekaru dubu biyu daga Yesu ya sami basira mafi kyau ga abin da Yesu Ya koyar masu da kansa (Yahaya 14:26)?
Me yasa tambayar kan gaskiyar shaidar Yesu tana da muhimmanci? Me yasa ya zama da al’amari ko dai a ce ko kada a ce Yesu Allah ne? Dalili mafi muhimmanci cewa da Yesu ya zama Allah ita ce idan Shi ba Allah bane, da mutuwar sa bata isa ta biya hukuncin na zunuban dukan duniya ba (1Yahaya 2:2). Allah kaɗai ne ke iya biya irin hukuncin marar iyaka haka (Romawa 5:8; 2 Korantiyawa 5:21). Sai da Yesu ya zama Allah don ya iya biya bashin mu. Sai da Yesu ya zama mutum don ya iya mutuwa. Ceto tana nan a yalwace kaɗai ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi! Allahntakar Yesu shine dalilin da yasa Shine kaɗai hanyar ceto. Allahntakar Yesu shine ya sa yayi shela, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina” (Yahaya 14:6).
English
Wane ne Yesu Kiristi?