Tambaya
Ɗazu na sa bangaskiya ta cikin Yesu… yanzu menene?
Amsa
Ɗazu na sa bangaskiya ta cikin Yesu… yanzu menene?
Barka da samun arziki! Ka yanke shawara mai canza –rayuwa! Watakila kana ta tambaya, “yanzu menene? Yaya zan iya fara tafiya ta tare da Allah?” Matakai guda biyar da aka ambace su a ƙasa zasu baka manufa daga Littafi Mai Tsarki. Yayinda kana da tambayoyi kan tafiyarka, don Allah a ziyarci www.GotQuestions.org/Hausa.
1. Ka tabbatar ka gane da ceto
1Yahaya 5:13 tana gaya mana, “ Na rubuto maku wannan ne, ku da kuka gaskata da sunan Ɗan Allah, domin ku tabbata kuna da rai madawwami” Allah yana son mu da mu gane da ceto. Allah yana son mu da mu zama da amincewa na sanin tabbas cewa an cece mu. A gurguje, bar mu bi kan mabuɗin manufofi na ceto:
(a) Dukanmu mun yi zunubi. Mu duk mun aikata abubuwan da basa gamsarwa ga Allah (Romawa 3:23).
(b) Domin zunubanmu, mun cancanta ayi mana hukunci da rabuwa na har abada daga Allah (Romawa 6:23).
(c) Yesu ya mutu bisa kan gicciye don ya biya hukunci na zunubanmu (Romawa 5:8; 2 Korantiyawa 5:12). Yesu ya mutu a madadinmu, ya ɗauke hukuncin da ya cancance mu. Tashinsa ta jarraba cewa mutuwar Yesu ce ta isa ta biya don zunubanmu.
(d) Allah yana biye gafartawa da ceto ga duk waɗannan waɗanda suka sa bangaskiyarsu cikin Yesu –suna amincewa da mutuwarsa a matsayin biyarwa ne don zunubanmu. (Yahaya 3:16; Romawa 5:1; Romawa 8:1).
Wannan ce saƙon ceto! Idan ka sa bangaskiyarka cikin Yesu Kiristi a matsayin mai cetonka, ka sami ceto! Dukan zunubanka an yafe su kuma Allah yayi alƙawari ba zai taɓa bar ka ko ya yashe ka ba (Romawa 8:38-39; Matiyu 28:20). Ka tuna, cetonka tana ɗaure ne cikin yesu Kiristi (Yahaya 10:28-29). Idan kana amincewa cikin Yesu kaɗai a matsayin mai cetonka, zaka iya sami tabbas cewa zaka yi zama na har abada tare da Allah cikin samaniya!
2. Ka nemi kyakkyawar ikilisiya mai koyar da Littafi Mai Tsarki.
Kada kayi tunanin ikilisiya da kamar gini ne. Ikilisiya ta zama mutane ne. Tana da muhimanci ainun cewa masu bin yesu Kiristi su yi zumunci da junasu. Ita ce ɗaya daga cikin manyan manufofin ikilisya. Yanzu da ka riga ka sa bangaskiyarka cikin Yesu Kiristi, muna ƙarfafa ka da ƙarfi da ka sami wata ikilisiya mai bada gaskiya ga Littafi Mai Tsarki a yankinku kuma kayi magana da wani fasto. Bar shi ya san game da sabuwar bangaskiyarka cikin Yesu Kiristi.
Manufa ta biyu game da ikilisiya ita ce a koyar da littafi Mai Tsarki. Zaka iya koyi yadda ake shafa umarnan Allah a rayuwarka. Ganewa da littafi Mai Tsarki shine mabuɗin rayuwar nasara da rayuwar Kirista mai ƙarfi. 2 Timoti 3:16-17 tana cewa, “Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci, domin bawan Allah ya zama cikakke, shiryayye sosai ga kowane kyakkyawan aiki.”
Manufa ta uku ta ikilisiya ita ce sujada. Sujada shine a gode wa Allah don dukan abin da Shi yayi! Allah ya cece mu, Allah na ƙaunar mu. Allah na tanada mana. Allah na bishe mu da kuma gwada mana. Yaya ba zamu iya gode masa ba? Allah mai tsarki ne, mai adalci, mai ƙauna, mai jinƙai kuma cike da alheri. Wahayin Yahaya 4:11 tana shela, “Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu, Ka sami ɗaukaka, da girma, da iko, Domin kai ne ka halicci dukan abubuwa, Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”
3. Ka keɓe lokaci waje ɗaya a kowace yini ka fuskance Allah
Tana da muhimanci ainun garemu mu kashe lokaci kowace yini a fuskance Allah. Yawancin mutane suna ƙira wannan “ lokacin tsit.” Waɗansu na ƙiranta “ salla ko addu’a,” domin ita ce lokacin da muke duƙufar da kanmu ga Allah. Yawanci sun fi son keɓe lokuta waje guda cikin safiya, waɗansu kuwa sun fi son maraice. Bai zama da kome ba ko menene kake ƙira wannan lokaci ko loton da kake yin ta. Abin al’amarin shine cewa kai kullayaumin ka kashe lokaci tare da Allah. Waɗanne abubuwa ne masu maida mana lokaci tare da Allah?
(a) Addu’a. Addu’a a sauƙaƙƙe shine zance da Allah. Yi magana da Allah game da abubuwan da sun shafe ka da matsalolinka. Ka tambaye Allah ya baka hikima da bishewa. Ka tambaye Allah ya tanada don bukatarka. Ka gaya ma Allah yawan ƙaunarka zuwa greshi kuma da yabawarka da dukan abin da yana yi maka. Abin da yake game da addu’a duka kenan.
(b) Karatun Littafi Mai Tsarki. Bugu da ƙari da an koyar maka da Littafi Mai Tsarki cikin ikilisiya, Sonde Skul, kuma/ko nazarin Littafi Mai Tsarki- kana bukatar karanta Littafi Mai Tsarki don kanka. Littafi Mai Tsarki ta ƙunshi dukan abin da kake bukata ka sani domin ka yi rayuwar Kirista mai nasara. Tana ƙunshe da bishewar Allah don yadda zaka yanke shawarwari masu hikima, yadda zaka san nufin Allah, yadda zaka hidimta wa waɗansu, da kuma yadda zaka yi girmar ruhaniya. Littafi Mai Tsarki maganar Allah ne zuwa garemu. Littafi Mai Tsarki asalinta shine umarnan aikin hannun Allah ta yadda zamu yi rayuwarmu cikin tafarkin da ta gamshe shi kuma suna ƙosarwa garemu.
4. Ka raya dangantaka tare da mutane waɗanda zasu iya taimake ka a ruhaniya.
1Korantiyawa 15:33 tana gaya mana, “Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.” Littafi Mai Tsarki tana cike da gargaɗai game da tasirin da “miyagun” mutane zasu iya samarwa akanmu. Kashe lokaci tare da waɗancan waɗanda suka ɗulmaya cikin ayyukan zunubi zai yi sanadin mu jarrabtu ta waɗancan ayyuka. Halaya na waɗancan waɗanda suna kewaye damu zasu “shafa” akan mu. Shine dalilin da yasa ya zama da muhimanci mu kewaye kanmu tare da waɗansu mutane waɗanda suna ƙaunar Ubangiji kuma suna miƙa kai gare Shi.
Ka ƙoƙarta ka sami aboki ko biyu, watakila daga ikilisiyarka, waɗanda zasu iya su taimake ka da su ƙarfafa ka (Ibraniyawa 3:13;10:24). Tambaye abokananka su ri’ke ka da alhaki a batun lokacin ka na tsit, ayyukanka, da tafiyarka tare da Allah. Ka tambaya idan zaka iya yi daidai haka nan dominsu ma. Wannan ba ma’ana ce zaka yanke ƙauna da dukan abokananka waɗanda basu san Ubangiji Yesu a matsayin mai cetonsu ba. Ci gaba da zama abokinsu kuma ka ƙaunace su. A sauƙaƙƙe ka sa su san cewa Yesu ya riga ya canza rayuwarka kuma ba zaka iya yi daidai duk abubuwan da dă kun saba yinsu. Ka roƙi Allah ya baka damar tattauna Yesu tare da abokanka.
5. Kayi Baftisma
Yawancin mutane suna da rashin ganewa game da baftisma. Kalmar “baftisma” na nufin a nutsar cikin ruwa. Baftisma ita ce hanyar Littafi Mai Tsarki ta shaida a fili sabuwar bangaskiya cikin Yesu da miƙa kanka zaka bi shi. Aikin nutsarwa cikin ruwa tana kwatanta binnewa tare da Kiristi. A yayin fitowa daga cikin ruwa na nuna hoton tashin Kiristi ne. Ayi baftisma shine shaidar kanka tare da mutuwar Yesu, binnewa, da tashinsa (Romawa 6:3-4).
Baftisma ba ita ce abin da ta cece ka ba. Baftisma ba ta wanke zunubanka daga nan ba. Baftisma a sauƙaƙƙe dai mataki ne na biyayya, shaidar fili na bangaskiyarka cikin Kiristi kaɗai domin ceto. Baftisma tana da muhimanci don ita ce mataki na biyayya – ayi shelar bangaskiya cikin Kiristi a bainar jama’a da miƙa kanka gare shi. Idan kana a shirye don ayi maka baftisma, sai kayi zance tare da wani fasto.
English
Ɗazu na sa bangaskiya ta cikin Yesu… yanzu menene?