settings icon
share icon
Tambaya

Mene ne zai sa ba zan iya kashe kaina ba?

Amsa


Zuciya na je wurin waɗancan da suna da tunani su ƙare rayukansu ta wurin kisan kansu. Idan haka ne kake yanzu nan, mai yiwuwa kana ji a zuciya da yawa, kamar ji irin su rashin bege da fid da rai. Mai yiwuwa kaji kamar kana cikin zurfafan rami, kuma kana shakka akwai wata haske na sa rai cewa abubuwa zasu iya kyautatuwa. Ba wani da alama ya damu ko ya gane inda kake tahowa. Rai kawai bata cancanci rayuwa ba --- ko dai?

Da yawa suna ji da raunin zuciya a wasu lokatai ko wata.Tambayoyin da sun zo tunani na sa’anda nake cikin ramin tunanin zuci sune, “Ko wannan zai iya zama nufin Allah, wane ne ya halicce ni?” “ Ko Allah ya ƙaƙanta ya taimake ni?’ “Ko matsaloli na sun fi girman Sa?”

Ina da murna in gaya maka cewa idan zaka ɗauki ɗan lokaci ka duba da yardar wa Allah da gaske ya zama Allah cikin ranka yanzu nan, zai tabbatar da gaske yadda Shine babba! “Ba wata faɗar Allah da zata kasa cika” (Luka 1:37). Mai yiwuwa tabbai daga ciwo na dă suna da sakamako gaggaruma rashin karɓa ko yar wa. Wannan zai kai ga rashin mutunta kai, fushi, ɗacin rai, tunanin ramako ko hanyoyi, tsoro marar tushe, da sauransu, waɗanda suka kawo matsaloli cikin yawancin dangantakar ka mafi muhimmanci. Duk da haka, kisan kanka zai zama kaɗai ya jawo ɓarna ga kaunatattun ka da baka taɓa yi niyyar cutarwa ba; su yi fama da tabban zuciya na sauran rayuwar su.

Me yasa ba zaka kashe kan ka ba? Aboki, ko da yaya abubuwa sun lalace a cikin rayuwar ka, akwai wani Allah na ƙauna wanda yake jiranka ka yarda Shi ya bishe ka ta bututun fid da rai, kuma zuwa cikin hasken sa mai ban mamaki. Shine tabbataccen begen ka. Sunan sa Yesu ne.

Wannan Yesu, Ɗan Allah marar zunubi, yana tare da kai cikin loton ƙiyayya da cin mutunci. Annabi, Ishaya ya rubuta game dashi, “Bashi da wani makami ko kyan gani da zai sa mu kula da shi. Ba wani abin da zai sa mu so shi, ba kuma abin da zai ja mu zuwa gare shi. Muka raina shi, muka ƙi shi, ya ɗaure da wahala da raɗaɗi. Ya ɗaure da wahala. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome bane. Amma ya ɗaure da wahala wadda ta ainihi ta mu ce, raɗaɗin ya kamata mune zamu sha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa hukunci ne Allah yake yi masa, amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya ƴantar da mu, dukan da aka yi tayi masa, yasa muka warke. Dukan mu muna kama da tumaki da suka ɓata, kowannen mu ya kama hanyar sa. Sai Ubangiji yasa hukunci ya auko a kansa, hukuncin da ya wajaba a kanmu” (Ishaya 53:2-6).

Aboki, duk wannan Yesu ya jure garin mai yiwuuwa ka sami gafarar dukkan zunuban ka! Ko mece ce nauyin zunuban ka da kake ɗauke tare da kai, ka san cewa zai gafarta maka idan cikin tawali’u ka tuba (juyo daga zunuban ka, ga Allah). “Kuyi kira gare ni sa’adda wahala ta zo, zan cece ku (ƴantar da ku), ku kuwa zaku yabe ni” (Zabura 50:15). Babu abin da ka taɓa yi da yafi muni don Yesu ya gafarta. Yawancin bayin sa masu kirki a cikin Littafi Mai Tsarki sun aikata zunubai barkatai, kamar, kisan kai (Musa) zina (Sarki Dawuda), da cin mutuncin jiki da motsin rai (Manzo Bulus). Duk dai, sun sami gafara da sabuwar yalwar rai cikin Ubangiji. “Ka wanke mugunta ta sarai, ka tsarkake ni daga zunubina! (Zabura 51:2). “Saboda haka, duk wanda ke na Almasihu,sabuwar halitta ne, tsohon al’amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo” (2 Korantiyawa 5:17).

Me yasa ba zaka kashe kanka ba? Aboki, Allah na tsaye a shirye ya gyarta abin da ya fashe “---kamar, rai da kake da shi yanzu, da kake so ka ƙare ta kashe kan ka. Annabi Ishaya ya rubuta: “ Ubangiji ya saukar mani da ikonsa.Ya zaɓe ni, ya aike ni domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, in warkar da waɗanda suka karai a zuci, inyi shela kwance ɗaurarru, da kuma ƴanci ga waɗanda ke cikin kurkuku. Ya aike ni inyi shela, cewa lokaci yayi, da Ubangiji zai ceci mutanensa, ya kuma ci nasara a kan abokan gaban su. Ya aike ni domin in ta’azantar da masu makoki. Domin in kawo wa masu makoki --- farin ciki da murna (rawani mai ƙawa) maimakon bakin ciki, waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, zasu ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da ke daidai, za a yi yabon Allah saboda abin da yayi” (Ishaya 61:1-3).

Kazo gun Yesu, ka yardar masa ya maido da farin cikin ka da tasirinka yayin da ka amince da Shi ya fara sabuwar aiki a rayuwar ka. “Ka sake mayar mani da farin ciki na ceton ka, ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya. Baka son sadakoki, ai, da na baka, baka jin daɗin hadayun ƙonawa. Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah, zuciya mai ladabi da biyayya, ba zaka ƙi ba, Ya Allah.” (Zabura 51:12,15-17).

Ko zaka karɓi Ubangiji a matsayin mai ceto da makiyayin ka? Zai bi da tunani da matakan ka, kowace rana, ta maganarsa, Littafi Mai Tsarki “Zan koya maka hanyar zaka bi, zan koya maka, in kuma baka shawara” (Zabura 32:8). “Zai kuma sa aminci cikin al’ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama’arsa ya kuma basu hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji” (Ishaya 33:6). Cikin Kiristi, har yanzu zaka sami gwagwarmaya, amma yanzu zaka sami BEGE. Shine “abokin da yafi ƴan’uwa aminci” (Misalai 18:24). Bar alherin Ubangiji Yesu ya bi tare da kai cikin sa’arka na yanke shawara.

Idan kana da sha’awar amince da Yesu Kiristi a matsayin mai ceton ka, ka faɗi waɗannan kalmomi cikin zuciyar ka ga Allah. “Allah, ina bukatar ka cikin rayuwar ta. Don Allah ka gafarta mani dukkan abin da na aikata. Na sa bangaskiyata cikin Yesu Kiristi kuma na gaskata cewa shine mai cetona. Don Allah ka wanke ni, kuma ka maido da farin ciki a rayuwata. Na gode maka don ƙaunarka domina da kuma mutuwar Yesu a madadina.”

Ko ka yanke shawara domin Kiristi saboda abin da ka karanta anan? Idan haka ne, don Allah danna kan “Na riga na karɓi Kiristi yau” botin na ƙasa.

English



Koma zuwa shafin gida na Hausa

Mene ne zai sa ba zan iya kashe kaina ba?
© Copyright Got Questions Ministries